Powered By Blogger

Saturday, 10 December 2016

YADDA AKE RUQYA A MUSULUNCI.

dafarko dai kusani ruqya a musulunci halal ne manzon allah (s.a.w) yayi ruqya, ankarbo daga dan abbas (R.A) cewa wata taje wajen manzon allah tare da danta marar lafiya mai cutar hauka tace ya ma,aikin allah wannan yaronane yana damunmu da ta,adi da barna sai annabi ya dafa kirjin yaron yayimasa ruqya kuma yabuda bakinsa yayimasa toti aciki sai akaga wani abu baki wulik yafito daga bakin yaron take yatashi yasamu sauki ahmad da darumi ne suka rawaito hadisin KA,IDODIN RUQYA Wajen da za,ayi ruqya yakasance mai tsarki wurin yakasance babu kowa daga marar lafiya sai danginsa, idan macece dolene ta saka hijabi da dogon wando dan kar aljani yabaiyana ya bude mata tsiraici kayiwa marar lafiya da danginsa bayanin kai mai addu,a ne kawai, amma waraka tana wajen allah, afitar da duk wani photo dayake cikin dakin, ko yar tsana ko gunki ko wani zani mai almar foton mutum, domin duk wayannan abubuwa suna hana shigowar mala,iku (hadith) akarbe duk wani abu dayake jikin marar lafiya wanda yasabawa shari,a. GA ABINDA AKAFISO AKARANTA A RUQYA DAGA AYOYIN AL-QUR,ANI Amma wajibine kasani cewa dukkan ayoyin al-qur,ani warakane ga mutane ta,awizi da basmala fatiha aya 5 ta farkon suratul bakara ayoyi 2 tsakiyar suratul bakar, daga (wa ilahukum ilahuwahid), amanar rasulu akarshen suratul bakara, shahidallahu acikin suratul alimran daga aya ta 18-19 inna rabbakumullah, acikin suratul a,araf aya ta 54-56 afa hasibtum, suratul muminin aya ta 115-118 wa annahu ta,ala, suratul jinni aya ta 3-9 aya 10 na farkon suratul saffat, aya uku na karshen suratul hashri, aya ta 21-23 kulhuwallahu da falaki da nasi 3-3.,, domin annabi (s.a.w) yayi amfani da wadannan ayoyi ga marar lafiya kuma yasamu waraka amma inkaso zaka,iya amfani da qur,ani dukkansa waraka ne.... Muhdu a darasi nagaba

Daga taskar
Dr kabeer gidanmagani
08096343188, 08165341087
mkabeer5618@gmail.com
Www.gidanmagani.wordpress.com
Www.gidanmagani.blogspot.com

No comments:

Post a Comment