Powered By Blogger

Tuesday, 13 December 2016

FA'iDAR ZUMA DAGA ALQUR'ANI DA HADISI

FA'IDAR ZUMA DAGA AL-QUR'ANI DA HADISI

assalamau alaikum wa rahmatullah kuna tare Dr kabeer ishaq  gidanmagani
Insha Allah ayanzu zanyi karin bayanai akan zuma da irin abubuwab da zuma yakunsa dakuma fa'idodinta

(1)Allah yace abinsha yana fitowa daga cikinta mai launi launi acikinsa akwai magani ga mutane.
Manzon Allah (s.a.w) yace na horeku da waraka gUda 2 ZUMA DA ALQUR'ANI

(2) ABINDA ZUMA YA KUNSA ☆
zuma yakunshi sinadarin JALOZ acikinsa yakai 80% wannan sinadari yana tsotse cutat sikari (diabetes) 80% batare da shan wata wahala ba.
Sannan akwai gishirin ma'adinai acikin zuma sannan yakunshi vitamins, da burotayen da nau'o in mai kalakala.

MATSAYIN KUDAN ZUMA ☆
cikin taron kudan zuma gabadaya babu mai kasala suna aiki koda yaushe cikin nishadi  kuma kowacce akwai aikin da takeyi acikin dandazon kudan zuma akwai sarauniya da masu biyayya ga sarauniya akwai masu gini akwai masu tsaro da dai sauransu .

ZUMA ABICI NE MAI DARAJA☆
shan zuma gram 100 yana bawa ciki kuzari 300 wanda shi akeso mutum yasamu
Hakan ne yakesawa adore da lafiya kuma in an rasashi ne ake kamuwa da cututtuka iri iri musamman yara.
Haka  kuma kilo daya na zuma amfaninsa daidai yake da kilo 5 na madara haka kuma daidai yake da ayaba maikyau guda 26 kuma daidai yake da lemon zaki guda 60 kuma daidai yake da kwai guda 50 sannan daidai yake da nama kilo 11 kuma daidai yake da kayan rafi kilo 12  saboda haka yarage gareka mai hankali kanemi waraka da ZUMA......

MUHADU A DARASI NA 2 Daga taskbar
Dr kabeer ishaq
08096343188 08165351087
mkabeer5618@gmail.com
Ko a aziyarci shafukan mu na internet
Www.gidanmagani.wordpress.com kokuma www.gidanmagani.blogspot.com

No comments:

Post a Comment