Powered By Blogger

Monday, 5 December 2016

WANKAN GAWA DA YADDA AKEYINSA

DON ALLAH MU KARANTA KUMA MU YI
SHARING DA 'YAN UWA
, DOMIN NAKARANCI YAZAMA MATSALA
TA WANNAN AL'UMMA IDAN ANYI MUTUWA SAI KAGA AN RASA
MAIYIN WANKA,KO
KUMA KAGA MALAMIN DAZAIYI WANKAN
YANA TA MULKI SAIO
LOKACIN DAYAGA DAMA ZAI ZO YAYI
WANKAN.
ASSALAMU ALAIKUM
FALALAR WANKAN GAWA
Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda
Manzon Allah(S.A.W)
Yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke
mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau
arba’in.’’
A wani hadisin kuma Manzon Allah(S.A.W)
Yace, ”Duk wanda ya
wanke mamaci kuma ya rufa masa asiri, to
Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljanna
Kwarra (wato Launin
Tufafin)..

SHARUDDAN WANKAN GAWA
Daga cikin sharaddan wankan gawa sune:
1. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto
makusantan sa (misali, Iyaye,ko kanne,ko
yayye, ko “ya”ya, da
sauransu)
2. Ana bukatar maza su jibinci wanke
maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya
wanke Matarsa hakama
Mace zata iya wanke Mijinta)
3. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da
ruwan zafi.

YADDA AKE YIN WANKAN GAWA Ana yin wankan gawa mara-mara ne
(misali, Sau Uku(3) ko
Biyar(5) ko Bakwai(7) ko Tara(9)).
Hakan
ya tabbata daga
Manzon Allah (S.A.W) a cikin hadisin
Ummu Adiya(R.A). Wadanda zasu yiwa mamaci wanka su
zasu yi la’akari suga
wanka nawa ya dace suyi masa.
Da farko dai kafin a fara wankan da akwai
abubuwa guda Uku(3)
da za’a fara yiwa mamacin. Sune kamar haka:
1. Za’a cire masa suturar da take jikinsa,
amma za’a sami dan
kyalle a rufe masa al’aurarsa.
2. Bayan anyi abu na sama, sai kuma ayi
masa tsarki,na bangaren mafuta biyu.(Bawali da Gayadi)
3. Idan mace ce , za’a tsefe kitsan da yake
kanta, a wanke kan,
sannan ayi Lallabi uku a kan ( wato Kalba
guda Uku). Sai a
kwantar da Kalbar tayi bayan kan nata. Idan namiji mai kitso ne sai a warware
kitson gabadaya

YADDA AKE WANKA SAU UKU (3)
Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi
suyi masa wanka sau
uku, to bayan sun gama abubuwan da suke sama sai su fara
wankan...
Da farko dai zasu tanadi ruwa
kashi Uku (3), kowanne ruwa za
ayi wanka daya dashi.

WANKAN FARKO (RUWAN FARKO)
Wannan wankan za ayi wa mamaci ne wanka irin Wankan
Janaba.
Da farko za’a fara yiwa mamaci alwala ne,
kamar irin alwalar
Sallah, sai dai wajen kuskurar baki da
shakar hanci za’a shafa masa ruwa ne kawai a bakin da hancin.
Bayan anyi masa alwala, sai kuma a zuba
ruwa a kansa a wanke
masa har sau uku, sannan kuma a wanke
tsagin jikinsa na dama
sannan na hagu.

WANKA NA BIYU (RUWA NA BIYU)
Bayan anyi masa wanka na sama wato na
Janaba, sai kuma a
sami Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a
wanke mamacin dashi.
Wato za’a sami Soso da Sabulu a cuda jikinsa sosai (Kamar dai
yadda ake wanka irin na Soso da Sabulu,
sai dai za’a iya amfani
da Magarya ko Kanwa a maimakon
Sabulun).
Bayan an gama
cuda shi sai a dauraye Kumfar da wannan ruwan.

WANKA NA UKU (RUWA NA UKU)
Bayan anyi masa wanka na sama, wato na
Soso da Sabulu, to
sai kuma a sami ruwa na karshe wato na
Uku a zuba Turare me kamshi(Sosai) a ciki, sannan sai a wanke
mamaci da shi.
Amfi son ayi amfani da Turaren Kafur, to
amma idan ba’a same
shi ba to za’a iya amfani da duk wani
Turare mai kamshi sosai Bayan an gama wankan Turaren, to sai a
tsane jikin mamacin a
sa masa Likkafani.

YADDA AKE YIN WANKA BIYAR (5), KO
BAKWAI (7), KO TARA (9)
Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi su yiwa masa wanka
biyar(5),ko bakwai(7), ko tara(9), to
wanka na biyu(2) wato na
Soso da Sabulu shi zasu ta maimaitawa.
Amma dole ne na Janaba shi ne a Farko,
sannan na Turare shi ne a karshe.

MISALIN YADDA ZA AYI WANKAN SAU
BIYAR (5)
1. Na farko shi ne na Janaba
2. Na biyu shi ne na Soso da Sabulu
3. Na Uku shi ne na Soso da Sabulu 4. Na Hudu shi ne na Soso da Sabulu
5. Na Biyar shi ne na Turare.

Daga taskar
Dr kabeer ishaq

No comments:

Post a Comment