HALITTAR JINNU. Jinnu halitune da allah ta,ala yayi domin subauta masa yakuma ajiyesu a duniya, kuma allah ya haliccesu daga harshen wuta allah yace "kuma yahalitta aljani daga (BIRA) ta wuta (harshen wuta) dan abbas yace lallai aljanu anhaliccesu daga harshen wuta. Dan haka sai muce jinnu wasu halittune da allah yahaliccesu daga harshen wuta shiyasa ba,a ganinsu kuma ba,a iya tabasu ko jin motsinsu, saboda su ruhine kawai basuda tabbataccen gangar jiki irinna dan adam shiyama suke iya rikida izuwa duk surar da sukaga dama, kamar kare, maciji, kyanwa, da sauran halittu.. Allah ta,ala ya halicci jinnu nau,in halittu mabambanta. Hakim yarawaito hadisi daga aba sa,alatal kushaniyya yace manzon allah (s.a.w) yace aljanu nau,i ukune, akwai masu fuka fukai suna tashi sama, da masu zama macizai da kunamai, da kuma masuzama waje daya su kaura.
Daga taskar
Dr kabeer Gidanmagani
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com
Www.gidanmagani.wordpress.com
Www.gidanmagani.blogpost.com
No comments:
Post a Comment