Powered By Blogger

Tuesday, 13 December 2016

ZAITUN DA AMFANINSA

🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿
ZAITUN DA AMFANINSA
🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿🌿

assalam alaikum yan uwana mutanen wannan group inayimaku fatan alkhairi  nine kabeer ishaq ayauma kamar kullun insha allah zamuyi kokarin kawo maku fa, idodin ZAITUN 🌿
Hakika zaitun yana daga cikin itatuwa masu daraja domin allah s. w. t yayi rantsuwa da zaitun acikin al-qurani maigirma 📖

1⃣ GAME DA MAI FAMA DA KARANCIN JINI AJIKINSA
sai yasamu yayan zaitun arika cin guda 6 arena.
2⃣ GAME DA MAI FAMA DA BASUR
asamu zaitun ahada da sassaken danya arika sha anono ko kunu ko ma aruwa 
3⃣ GAME DA CHIWON MARA NA MATA
Asamu man zaitun ahada da ruwan tsamiya arika sha za, asamu sauki insha allah.
4⃣ GAME DA SANYIN KASHI
Asamu man zaitun ahada da man habbatussauda  arika sha ana shafawa awajen da yake ciwon.
5⃣ GAME DA GYARAN FATA TAYI LAUSHI DA KYAU
Arika wanka da ruwan dumi sannan in an fito ashafe jiki da man zaitun ✅✅✅
Zantsaya ahaka sabida saukin karantawa muhadu a darasi na 2 

🙏🏼🙏🏼Dr kabeer ishaq 🙏🏼🙏🏼
08096343188

FA'iDAR ZUMA DAGA ALQUR'ANI DA HADISI

FA'IDAR ZUMA DAGA AL-QUR'ANI DA HADISI

assalamau alaikum wa rahmatullah kuna tare Dr kabeer ishaq  gidanmagani
Insha Allah ayanzu zanyi karin bayanai akan zuma da irin abubuwab da zuma yakunsa dakuma fa'idodinta

(1)Allah yace abinsha yana fitowa daga cikinta mai launi launi acikinsa akwai magani ga mutane.
Manzon Allah (s.a.w) yace na horeku da waraka gUda 2 ZUMA DA ALQUR'ANI

(2) ABINDA ZUMA YA KUNSA ☆
zuma yakunshi sinadarin JALOZ acikinsa yakai 80% wannan sinadari yana tsotse cutat sikari (diabetes) 80% batare da shan wata wahala ba.
Sannan akwai gishirin ma'adinai acikin zuma sannan yakunshi vitamins, da burotayen da nau'o in mai kalakala.

MATSAYIN KUDAN ZUMA ☆
cikin taron kudan zuma gabadaya babu mai kasala suna aiki koda yaushe cikin nishadi  kuma kowacce akwai aikin da takeyi acikin dandazon kudan zuma akwai sarauniya da masu biyayya ga sarauniya akwai masu gini akwai masu tsaro da dai sauransu .

ZUMA ABICI NE MAI DARAJA☆
shan zuma gram 100 yana bawa ciki kuzari 300 wanda shi akeso mutum yasamu
Hakan ne yakesawa adore da lafiya kuma in an rasashi ne ake kamuwa da cututtuka iri iri musamman yara.
Haka  kuma kilo daya na zuma amfaninsa daidai yake da kilo 5 na madara haka kuma daidai yake da ayaba maikyau guda 26 kuma daidai yake da lemon zaki guda 60 kuma daidai yake da kwai guda 50 sannan daidai yake da nama kilo 11 kuma daidai yake da kayan rafi kilo 12  saboda haka yarage gareka mai hankali kanemi waraka da ZUMA......

MUHADU A DARASI NA 2 Daga taskbar
Dr kabeer ishaq
08096343188 08165351087
mkabeer5618@gmail.com
Ko a aziyarci shafukan mu na internet
Www.gidanmagani.wordpress.com kokuma www.gidanmagani.blogspot.com

Saturday, 10 December 2016

YADDA AKE RUQYA A MUSULUNCI.

dafarko dai kusani ruqya a musulunci halal ne manzon allah (s.a.w) yayi ruqya, ankarbo daga dan abbas (R.A) cewa wata taje wajen manzon allah tare da danta marar lafiya mai cutar hauka tace ya ma,aikin allah wannan yaronane yana damunmu da ta,adi da barna sai annabi ya dafa kirjin yaron yayimasa ruqya kuma yabuda bakinsa yayimasa toti aciki sai akaga wani abu baki wulik yafito daga bakin yaron take yatashi yasamu sauki ahmad da darumi ne suka rawaito hadisin KA,IDODIN RUQYA Wajen da za,ayi ruqya yakasance mai tsarki wurin yakasance babu kowa daga marar lafiya sai danginsa, idan macece dolene ta saka hijabi da dogon wando dan kar aljani yabaiyana ya bude mata tsiraici kayiwa marar lafiya da danginsa bayanin kai mai addu,a ne kawai, amma waraka tana wajen allah, afitar da duk wani photo dayake cikin dakin, ko yar tsana ko gunki ko wani zani mai almar foton mutum, domin duk wayannan abubuwa suna hana shigowar mala,iku (hadith) akarbe duk wani abu dayake jikin marar lafiya wanda yasabawa shari,a. GA ABINDA AKAFISO AKARANTA A RUQYA DAGA AYOYIN AL-QUR,ANI Amma wajibine kasani cewa dukkan ayoyin al-qur,ani warakane ga mutane ta,awizi da basmala fatiha aya 5 ta farkon suratul bakara ayoyi 2 tsakiyar suratul bakar, daga (wa ilahukum ilahuwahid), amanar rasulu akarshen suratul bakara, shahidallahu acikin suratul alimran daga aya ta 18-19 inna rabbakumullah, acikin suratul a,araf aya ta 54-56 afa hasibtum, suratul muminin aya ta 115-118 wa annahu ta,ala, suratul jinni aya ta 3-9 aya 10 na farkon suratul saffat, aya uku na karshen suratul hashri, aya ta 21-23 kulhuwallahu da falaki da nasi 3-3.,, domin annabi (s.a.w) yayi amfani da wadannan ayoyi ga marar lafiya kuma yasamu waraka amma inkaso zaka,iya amfani da qur,ani dukkansa waraka ne.... Muhdu a darasi nagaba

Daga taskar
Dr kabeer gidanmagani
08096343188, 08165341087
mkabeer5618@gmail.com
Www.gidanmagani.wordpress.com
Www.gidanmagani.blogspot.com

DALILAN DA YASA JINNU SUKE SHAFAR MUTUM

akasarin jinnu suna shafjr mutum ne saboda daya daga cikin wadannan dalilai dasunan kauna ko ma aure ga mace ko namiji saboda zalunci da mugunta saboda zaluncin da dan adam yayimusu kamar zuba ruwan zafi ko yatakasu idan bokaye da matsafa sun turosu.. LOKATAN DA JINNU KE SHIGA JIKIN DAN ADAM. lokacinda mutum yatsorata, lokacinda mutum yake cikin matsanancin bacin rai da fushi, lokacinda mutum ya nutse cikin sabon allah kamar kallace kallacen finafinan batsa, lokacin da mutum ya nutse cikin tsananin nishadi da masha,a, lokacinda mutum yake cikin janaba ko haila ta mata... ALAMOMIN SAMUWAR ALJANU AJIKIN DAN ADAM Yawan mantuwa mai tsanani, samun damuwa da kuncin rai mutuwar wani bangare najikin mutum cizon hakori a barci, jin wani motsi kamar anabinka abaya yawan kokwanto firgita abarci, yawan mafarkin saduwa babisa ka,idaba yawan zubar jinin haila ba ka,ida jin sauti kamar ana kiranka, da makamantansu

Saga taskar
Dr kabeer gidanmagani
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com
Www.gidanmagani.wordpress.com
Www.gidanmagani.blogspot.com

MATSALAR ALJANNU DA RUQYA

HALITTAR JINNU. Jinnu halitune da allah ta,ala yayi domin subauta masa yakuma ajiyesu a duniya, kuma allah ya haliccesu daga harshen wuta allah yace "kuma yahalitta aljani daga (BIRA) ta wuta (harshen wuta) dan abbas yace lallai aljanu anhaliccesu daga harshen wuta. Dan haka sai muce jinnu wasu halittune da allah yahaliccesu daga harshen wuta shiyasa ba,a ganinsu kuma ba,a iya tabasu ko jin motsinsu, saboda su ruhine kawai basuda tabbataccen gangar jiki irinna dan adam shiyama suke iya rikida izuwa duk surar da sukaga dama, kamar kare, maciji, kyanwa, da sauran halittu.. Allah ta,ala ya halicci jinnu nau,in halittu mabambanta. Hakim yarawaito hadisi daga aba sa,alatal kushaniyya yace manzon allah (s.a.w) yace aljanu nau,i ukune, akwai masu fuka fukai suna tashi sama, da masu zama macizai da kunamai, da kuma masuzama waje daya su kaura.

Daga taskar
Dr kabeer Gidanmagani
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com
Www.gidanmagani.wordpress.com
Www.gidanmagani.blogpost.com

Friday, 9 December 2016

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA KASH NA2I

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA (iyayen giji ) 2

Idan mace tana bukatar maniyinta yakaru, sai tasami madarar shanu kofi 1 tazuba man tafarnuwa karamin cokali 3 tasha sau 2 arana zata samu karin ni,ima nantake tabaiwa megida mamaki. MATAR DA TAKESO GABANTA YA MATSE; tasami wani turare maisuna (misk al-gazali) daya bisa hudu na karamin cokali ahada da man tafarnuwa karamin cokali atsoma auduga tasa agabanta tayi kunzugu ayihaka kwana 4 ko 5, zatakoma kamar budurwa...@{ amma aji tsoron allah}..

Daga taskar
Dr KABEER ISHAQ

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA (iyayen giji)

Gaeme da matarda bata taba haihuwaba idan tanaso tagane zata iyasamun ciki? Ko a,a? To sai tasamuwa mai dumi da sabulu tawanke gabanta sosai sannan tasamu auduga maikyau sannan tazuba man tafarnuwa cokali daya akan audugar sannan tayi kunzugu da audugar har tsawon awa 2, intaji warin tafar nuwar abakinta, zatasamu ciki lokacine baiyiba kokuma matsalar daga mijinne inkuma batajiba to sai dai allah yasawake, amma ana maimaitawa har sau uku domin kara tabbatarwa.. YAWAN LALACEWAR CIKI KO YAWAN BARI; asamu kwan agwagwa asoya da man tafarnuwa abaiwa matar taci sau 2 arana kwana 7. TSAWON GASHI DA HANASHI KAKKARYEWA; Asamu man kwakwa ahada da man zaitun da man tafarnuwa arinka shafawa akai, amma man tafarnuwa 50% za,asa sauran kuma 100&... Allah yasa mudace...

DAGA TASKAR
Dr kabeer ishaq
08096343188, 08165351087
mkabeer5618@gmail.com

AMGANIN MAN TAFARNUWA GA MAZA

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MAZA

idan namiji yanajin kaikayi a marainansa ko a azzakarinsa to sai yasamu garin farar kanwa cokali 1 adafa da ruwa kofi 2 idan ya tafasa sai azuba man tafarnuwa cokali 2 inyahuce sai yawanke gabansa da ruwan zaisamu sauki insha allah

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com

ABUBUWAN DA SUKE HANA DAUKAN CIKI


assalamu alaiku wa rahmatullah
In ANAS0 agane dalilin dayakan hana samun ciki ana ganowa ta hanyoyi da dama zamu fadi kadan dagaciki.
(1) idan al aurar namiji yacika kankanta wani lokacin yanahana samun ciki.
(2) idan yanayin al,aurar namiji yacanza ta yadda maniyi bayafutowa sai dakyar yanahana samun ciki.
(3)damuwa mai tsanani ko rashin kxanciyar hankali ga mace yana hanata samun ciki
(4)idan mace tana yawan yin kaho yana hanata daukan ciki.
(5) idan akarasa dalilin rashin samun ciki sai ashuka dawa ko GER0 sai a umarci mace tarika yin fitsari akan wannan shuka idan shukar tafito to zata iya samun haihuwa inkuma batafitoba to sai addu,a. (wallahu a,alam)
(6) asamu kofi azuba ruwa acikinsa sannan azuba maniyin namiji acikin ruwan idan maniyin yataso saman ruwan to maniyin ba mai haihuwa bane sai anemi magani. wallahu a,alam
xantsaya anan muhadu a kashi na 2
<[=DR KABEER=]>

ABUBUWAN DA SUKE HANA DAUKAN CIKI KASHINA 2

ABUBUWAN DA SUKE HANA DAUKAN CIKI KASHINA 2

ABUBUWAN DA SUKE HANA SAMUN CIKI KASHINA 2
(7) Yawan fitar jinin haila yanahana daukan ciki domin yana sanyaya mahaifa tayadda in maniyi yashiga sai ya daskare. zamu fadi maganinsa nangaba insha allah.
(8) idan maniyi yazama dan kankani koyazama kamar ruwa ko yayi kauri dayawa yana hana samun haihuwa.
(9) idan mace tayi kunzugu da gishiri a lokacin da ta haihu kafain asadu da ita ko bayan ansadu da ita bazata samu cikiba.(10) idan mace tana kifa cikinta tayi rub da ciki bayan da akagama saduwa da ita wannan ma yanahana daukan ciki ko tauna danyen wake ko hadiyar yayan zurman...
zan tsaya anan insha allah zandora akan
ABUBUWAN DA SUKE TAIMAKAWA ASAMU CIki

<[=DR KABEER=]>.
96343188,08165351087
Mkabeer5618@gmail.com


ABUBUWA 6 DASUKE TAIMAKAWA MACE TA DAUKI CIKI (juna biyu)

g-m-3.jpg ABUBUWA 6 DA SUKE TAIMAKAWA MACE TA SAUMU CIKI (juna biyu) Assalamu alaikum wa rahmatullah (1) yin kunzugu (mace tasa yanki ko wani abu a kofar al,aurar ta) sai tasaka turare ko wani abu maidadin kamshi acikin tsumman kunzugun yin haka yana taimakawa asamu ciki. (2)saduwa da mace lokacin da batadade da gama al,ada ba hakan yana taimakawa asamu ciki domin mahaifarta tanada dumi alokaci. ¿ (3)idan mace tasha nonon taguwa (macen rakumi) in mijinta yasadu da ita za,a iya samun ciki in allah yaso. (4)idan mace tasamu garin habbatussauda mai laushi ta cakuda da manshanu tarika lasa lokacin da zatayi barci. insha allah zata samu ciki. (5)yin istigfari lokacin jima,i yanasawa mace tasamu ciki. (6) wanzamai sunce idan mace tasamu cibiyar jariri wacce take gutsirewa bayan anyi gashi sai ajikata acikin mai 24h sannan mace tayi kunzugu da ita awa 2 kafin jima,i. wannan ma yana taimakawa mace tadauki ciki... wassalamu alaikum wa rahmatullah
.
[<+=Dr [KABEER ISHAQ]=+>]
08096343188,08096343188165351087
mkabeer5618@gmail.com


MAGANIN CIWON MARA

%%CIWON MARAR MAI HAILA%% Mafiya yawa daga cikin mata na kuka da ciwon mara wanda kan hanawa wasu rawar gaban hantsi. So dayawa xakaga mace na xullumin tsayuwar wata domin tasan irin axabar datakesha duk adalilin ciwon mara. Ciwone dakan tsananta agurin wasu yakuma galabaitar dasu wasuma har amai xakaga sunayi yayin da wasu numfashinsu ke dauke yakaisu ga suma. La'akari dahakan yasa nima nafadada bincike domin kawo ma 'yan uwa mata wasu daga cikin hanyoyin daxasubi dan ganin Allah yasauwake yakuma basu lafia. 1.kisamu dabino masu kyau sabbin tsinka guda bakwai, kici dasafe kafin kici komai. 2.kisamu xogale kadan da tsamiya kisa akofi, sannan kisamu tafasashen ruwa kixuba akofin idan yadan huce kishanye alokacin. Kiyi haka har sau uku. Insha Allahu xaki samu sauki 3.kisamu dauwa kamar rabin mudu kijikata akwano natsawon kwana biyu sannan ki mutssiketa kitace sannan kisha. Yana maganin ciwon mara sosai yanakuma tsinka jini gawadda ciwon yadameta jini baixoba idan dai tai hakan jinin xaixo ciwon yayi sauki. Allah yabama masu fama da wannan matsalar lafiya ameen.

Daga taskar
Dr kabeer gidan magani
08096343188, 08165351087
Email mkabeer5618@gmail.com

Monday, 5 December 2016

WANKAN GAWA DA YADDA AKEYINSA

DON ALLAH MU KARANTA KUMA MU YI
SHARING DA 'YAN UWA
, DOMIN NAKARANCI YAZAMA MATSALA
TA WANNAN AL'UMMA IDAN ANYI MUTUWA SAI KAGA AN RASA
MAIYIN WANKA,KO
KUMA KAGA MALAMIN DAZAIYI WANKAN
YANA TA MULKI SAIO
LOKACIN DAYAGA DAMA ZAI ZO YAYI
WANKAN.
ASSALAMU ALAIKUM
FALALAR WANKAN GAWA
Al-Imam Hakim ya rawaito hadisi wanda
Manzon Allah(S.A.W)
Yake cewa: ‘’Duk wanda ya wanke
mamaci, kuma ya rufa masa asiri, Allah Zai gafarta masa sau
arba’in.’’
A wani hadisin kuma Manzon Allah(S.A.W)
Yace, ”Duk wanda ya
wanke mamaci kuma ya rufa masa asiri, to
Allah zai tufatar dashi daga cikin tufafin Gidan Aljanna
Kwarra (wato Launin
Tufafin)..

SHARUDDAN WANKAN GAWA
Daga cikin sharaddan wankan gawa sune:
1. Ana bukatar wadanda zasu wanke mamacin su zamanto
makusantan sa (misali, Iyaye,ko kanne,ko
yayye, ko “ya”ya, da
sauransu)
2. Ana bukatar maza su jibinci wanke
maza, suma mata su jibinci wanke mata (sai dai Miji zai iya
wanke Matarsa hakama
Mace zata iya wanke Mijinta)
3. Ba sharadi bane lallai sai anyi amfani da
ruwan zafi.

YADDA AKE YIN WANKAN GAWA Ana yin wankan gawa mara-mara ne
(misali, Sau Uku(3) ko
Biyar(5) ko Bakwai(7) ko Tara(9)).
Hakan
ya tabbata daga
Manzon Allah (S.A.W) a cikin hadisin
Ummu Adiya(R.A). Wadanda zasu yiwa mamaci wanka su
zasu yi la’akari suga
wanka nawa ya dace suyi masa.
Da farko dai kafin a fara wankan da akwai
abubuwa guda Uku(3)
da za’a fara yiwa mamacin. Sune kamar haka:
1. Za’a cire masa suturar da take jikinsa,
amma za’a sami dan
kyalle a rufe masa al’aurarsa.
2. Bayan anyi abu na sama, sai kuma ayi
masa tsarki,na bangaren mafuta biyu.(Bawali da Gayadi)
3. Idan mace ce , za’a tsefe kitsan da yake
kanta, a wanke kan,
sannan ayi Lallabi uku a kan ( wato Kalba
guda Uku). Sai a
kwantar da Kalbar tayi bayan kan nata. Idan namiji mai kitso ne sai a warware
kitson gabadaya

YADDA AKE WANKA SAU UKU (3)
Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi
suyi masa wanka sau
uku, to bayan sun gama abubuwan da suke sama sai su fara
wankan...
Da farko dai zasu tanadi ruwa
kashi Uku (3), kowanne ruwa za
ayi wanka daya dashi.

WANKAN FARKO (RUWAN FARKO)
Wannan wankan za ayi wa mamaci ne wanka irin Wankan
Janaba.
Da farko za’a fara yiwa mamaci alwala ne,
kamar irin alwalar
Sallah, sai dai wajen kuskurar baki da
shakar hanci za’a shafa masa ruwa ne kawai a bakin da hancin.
Bayan anyi masa alwala, sai kuma a zuba
ruwa a kansa a wanke
masa har sau uku, sannan kuma a wanke
tsagin jikinsa na dama
sannan na hagu.

WANKA NA BIYU (RUWA NA BIYU)
Bayan anyi masa wanka na sama wato na
Janaba, sai kuma a
sami Sabulu ko Magarya ko Kanwa, a
wanke mamacin dashi.
Wato za’a sami Soso da Sabulu a cuda jikinsa sosai (Kamar dai
yadda ake wanka irin na Soso da Sabulu,
sai dai za’a iya amfani
da Magarya ko Kanwa a maimakon
Sabulun).
Bayan an gama
cuda shi sai a dauraye Kumfar da wannan ruwan.

WANKA NA UKU (RUWA NA UKU)
Bayan anyi masa wanka na sama, wato na
Soso da Sabulu, to
sai kuma a sami ruwa na karshe wato na
Uku a zuba Turare me kamshi(Sosai) a ciki, sannan sai a wanke
mamaci da shi.
Amfi son ayi amfani da Turaren Kafur, to
amma idan ba’a same
shi ba to za’a iya amfani da duk wani
Turare mai kamshi sosai Bayan an gama wankan Turaren, to sai a
tsane jikin mamacin a
sa masa Likkafani.

YADDA AKE YIN WANKA BIYAR (5), KO
BAKWAI (7), KO TARA (9)
Idan masu yiwa mamaci wanka sun zabi su yiwa masa wanka
biyar(5),ko bakwai(7), ko tara(9), to
wanka na biyu(2) wato na
Soso da Sabulu shi zasu ta maimaitawa.
Amma dole ne na Janaba shi ne a Farko,
sannan na Turare shi ne a karshe.

MISALIN YADDA ZA AYI WANKAN SAU
BIYAR (5)
1. Na farko shi ne na Janaba
2. Na biyu shi ne na Soso da Sabulu
3. Na Uku shi ne na Soso da Sabulu 4. Na Hudu shi ne na Soso da Sabulu
5. Na Biyar shi ne na Turare.

Daga taskar
Dr kabeer ishaq

MATSALAR INPECTION


TOILET INFECTION ***************************** Idan ba toilet infection aka fada ba wasu ba zasu fahimci me ake nufi ba. Kamar yadda kuka sani "Infection" dai kalmar turanci ce wacce a hausance ma'anarta take nufin kamuwa da wata cuta To idan aka ce toilet infection ana nufin Ciwon da aka 'dauko a ban 'daki. Shi wannan ciwon aka sarin yafi kamuwar mata masu zuwa kai tsaye a toilet su du'ka su biya bukatarsu ba tare da tunani akan cewa kafin fa in gabatarda bukata ta a bayin nan bari in fara zuba ruwa, domin ban san wace irin cuta ce take daddabe a wannan bayin ba. To daga keyi wannan dukawar shikenan idan akwai irin wayannan bacterias nan take zasu shiga cikin al'aurar taki su haifar miki wannan mugun ciwo. Daga cikin hanyoyin da wannan mugun ciwo ke samuwar mafiyawan mata itace, hanyar shiga ban 'daki ba'a wanke hannu da Sabulu ko kasa ba. Irin wannan rashin wanke hannu da sabulu ko kasa yakansa hannun hagu yayi mu'amula da hannun dama daga kezo keci abinci ba tare da wanke hannu ba to fa shikenan wannan bacteria zata bi ta cikin bakin ki. Wasa da hannu a cikin Al'aura (fingering) yana daga cikin manyan matsalolin da ke kawo shi, domin mai yiwuwa hannun na dauke da bacteria, daga ansa ka hannun kai tsaye mutum ya kai bacteriar ne da kansa. Har wayau akwai Madigo (lesbians) yana daga cikin abinda ke haifar da wannan matsalar domin akwai wata kankanuwar kwayar cuta (parasitic organism) idan har wadda ake madigo da ita na dauke da ita to nan take zata shafawa 'yar uwarta wannan cutar. Zama da wando mai datti ko kuma ya kwana 2 a jiki shima yana haifarda wannan matsalar domin datti ko zufan mutum na iya 'daukar wayannan kwayoyin ya kaisu cikin al'aurar mace. da dai makamantan haka. insha allah zandora akan maganin da yadace mai wannan lalura tayi amfani dashi

daga taskar
Dr kabeer ishaq
mkabeer5618@gmail.com
08096343188 , 08165351087,
www.Facebook.com/gidanmaganin gargajiya


Thursday, 1 December 2016

AMFANIN TUFFA (Apple)

AMFANIN TUFFA (Apple) AJIKIN dan adam 1. TUFFAH (APPLE) Wannan dan itace na dauke da sinadarin ‘Vitamin C’ duk da dai sinadarin na cikinsa kadan ne amma akwai wasu sinadarai wadanda su ma aikinsu dai dai yake da wannan sinadarin a cikinsa. wanda suke haduwa su taimakawa hanji wajen kare shi daga cutar Daji wato ‘Cancer’ a Turance wanda a yau ake fama da ita a duniya. Yana kuma taimaka zuciya daga bugun da ya wuce ka’ida. Tuffah ko Apple yana taimakon dasashi wajen kare shi daga cinyewa ya karfafa hakori, ya kare harshe daga wata cuta da ake kira ‘Mouth Cancer,’ wato Cutar Dajin Baki. Haka kuma taunashi da hakori ba irin na yangayu sai an datsa da wuka ba yana taimakawa wajen haskaka hakori. Wanda ke fama da ciwon kai musamman na gajiya ko damuwa, yana iya fereye shi ya cinye banda bawon, ciwon kan zai sauka. Ga masu matsalar kumewar ciki za su iya goga shi a abin goga Kubewa da bawonsa, su murza ganyen na’a na’a, su tace ruwan su zuba akai su zuba Zuma cokali biyu, su rika shansa da safe kan su karya na sati guda in suka yi a jere da yardar Allah za su rabu da matsalar. Kowanne dan ita ce in aka yanka shi aka bar rabi, ya yi duhu amfaninsa ya kare amma Apple ya bambanta domin amfaninsa ba ya karewa indai ba rubewa ya yi ba. Don haka ko kin yanka sai, kika ga yayi ruwan kasa wato ‘Brown’ saboda ajiye shi da aka yi, in dai a waje ne rufaffe mai tsafta, to a yi amfani da shi

wassalam alaikum
Daga taskar
Dr kabeer ishaq
08096343188
08165351087
Mkabeer5618@gmail.com

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA YARA KANA

  idan yaro yakai wata uku da haihuwa anabashi man tafarnuwa rabin karamin cokali sau uku arana kwana uku zairabashi da danshi da tafiyar ruwa da cutar tamowa amma arinka hadawa da abinda zaisha kuma shafawa yaro man tafarnuwa a dasashinsa yana saukaka fitowar hakorin jariri mace mai goyo idan batada isashshen ruwan nono sai tasamu hantar karamar dabba tasoya tacinye zatasamu karin nono amma azuba cokali daya na man tafarnuwa acikin man suyar,  idan yaro yana kurga ,(wata tsutsace da take fitowa a dubura) ko in yana kuka marar dalili sai abashi man tafarnuwa rabin cokali sau 2 arana, idan anaso yaro yakasance cikin kuzari da koshin lafiya sai tarika zuba man tafarnuwa karamin chokali a abincinta...
Daga taskar Dr kabeer

08096343188
08165351087
Mkabeer5618@gmail.com