Powered By Blogger

Thursday, 9 August 2018

AMFANIN MAN ZAITUN

AMFANIN MAN ZAITUN

Shidai zaitun itaciyace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan Adam , kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninta acikin
ALKUR'ANI MAI GIRMA
haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan Manzon Allah (S.A.W)
an karbo daga sayyadina umar yana cewa Manzon Allah (S.A.W) yace kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi ajikinku, domin hakika shi yana daga acikin bishiya mai albarka.
(❀) tirmizi ne ya ruwaito
DAGA CIKIN AIKIN ZAITUN
́◉ ```KARFIN MAZAKUTA``` ◉
Duk mutumin da ya samu kanshi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa acikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum , insha Allah zai samu karfin mazakuta sosai
Kada ka gaji duk wani magani da kagani ka gwada zaka dace insha Allah

♡ ```CIWON CIKI``` ♡
Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma.
Yasamu kamar sati daya yana sha ko kina sha insha Allah

◇ ```CIWON KAI```◇
Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare insha Allah zai samu lafiya
◉ ```CIWON HAKORI```◉
duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya'yan habbatussauda ya sakasu acikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah.
① ```CIWON HANTA```①
duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare.

✿```CIWON DADASHI``` ✿
Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.
o・ ```CIWON SUKARI``` ・o
duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci insha Allah

△ ```CIWON ASMA``` △
duk mutumin da wannan ciwon ya kamashi ,to sai ya samu ganyen zaitun ko ya'yan sa ya dinga turara wa.

☆ ```CIWON KODA``` ★
duk mutumin da yake ciwon koda, to sai ya dinga shan man zaitun cikin cokali uku a Rana insha Allah.
★ ```CIWON BAYA``` ★
duk mutumin da yake ciwon baya, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda a kwaba ya dinga shafawa abayan insha Allah.
✿ฺ´```CIWON RAMA````✿ฺ
duk mutumin da yaga yana ramewa, to ya dinga shan man zaitun kullum cokali uku insha Allah zaiyi kiba.

□ ```ZAZZABI MAI ZAFI``` □
duk mutumin daya kamu da zazzabi mai zafi to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya sannan yana karanta ayatul kursiyyu sau 7 yana tofawa acikin yana shafe jikinsa dashi insha Allah.
✿ฺ ```KYAWUN FUSKA``` ✿ฺ
Duk mutumin da yake so fuskar sa tayi kyau, tayi fari Wanda bazai cutaddashi ba, to yadinga shafa man zaitun Dana habbatussauda in zai kwanta bacci bayan ya tashi da safe ya wanke da sabulun salo zai mamakin yadda fuskarsa data koma.

♡ ZUBEWAR GASHI. ♡
duk mutumin da gashinta baya futowa sosai ko in ya futo sai ya zube , to saita samu ruwan zafi ta wanne kanta dashi sannan bayan ya dan bushe saita zuba man zaitun a hannun ta, sai ta shafe kannata dashi gaba daya kullum.

□ KARANCIN JINI
duk mutumin da yake da karanci jini a jikinsa to sai ya dinga shan man zaitun cokali biyu a Rana.
◎BAYAN GIDA MAI KAURI◎
ロ゚BASUR duk mutumin da yake shan wahala in yazo zaiyi bayan gida, wani ma sai Yayi kuka saboda wahala, to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya kwaba sai ya turashi acikin duburarsa.
◍•CIWON MARA GA MATA•◍
duk matar da take haila tana fama da ciwon Mara saboda fitar jini in tana so ta samu saukin wannan ciwon ,saita samu man zaitun tana hadawa da ruwan tsamiya tana sha, insha Allah duk lokacin da zatayi haila bazai Mata ciwo ba.

◉◞SANYIN KASHI◟◉
duk mutumin da kashinsa yayi sanyi baya iya motsashi, to sai ya samu man zaitun da man habbatussauda ya dinga sha yana kuma shafawa a wajan insha Allah .
└★KYAWUN FATA DA LAUSHINTA★┐
Duk mutumin da yake so fatarsa tayi laushi da kyau, to sai ya sami man ya dinga shafe jikinsa dashi bayan Yayi wanka da ruwan dumi, zai yi mamaki yadda fatarsa zata koma insha Allah

•••♪ KURAJEN KARZUWA
duk mutumin da yake da karzuwa ko wasu kuraje ko sabon miki, to sai ya samu ganyan zaitun ya kirbashi ya hada da garin habbatussauda yana shafawa awajan har ya warke.
♪. •••••∆ CIWON KUNNE
duk mutumin da yake ciwon kunne, to sai ya Bari in zai kwanta bacci sai a dinga hada man zaitun Dana habbatussauda yana digawa a kunnensa insha Allah.
♪. ••••••¶ CUTAR KYASFI
duk mutumin da yake da KYASFI ajikinsa, to sai ya samu ganyen zaitun busasshe ,ya dakashi yayi laushi sai ya Jada shi da man zaitun ya cakuda, ya dinga shafawa a wajen lokacin da zai kwanta bacci.sai ya wanke

(^_^;) SHAFAR ALJANU•••√
duk mutumin da yake so ya rabu da aljanu, to ya dinga amfani da man zaitun saboda aljanu basa sonshi, shida habbatussauda
Da haka yana da kyau mutum ya lazimci amfani da su akowane hali, in da hali ma ya mai dasu mansa na shafawa amma yana da kyau kafin a Fara shafawa a karanta ayoyin rukya sai a nemi addu'a.
¶•••CIWON KARKARE•••¶
Duk mutumin da ciwon karkare yasa meshi, to sai ya samu man zaitun, sannan asamu lalle a kwaba, sai azuba man zaitun din acikin lalle a gauraya, sannan a karanta (AYATUL KURSIYYU) sau 7 a tofa a ciki sannan sai a tofa ajikin wannan karkare insha Allah
⌒CIWAN NONO⌒
Duk matar da take fama da ciwan nono saboda rashin zubar, to Ana hada man zaitun da garinsa, abarbada akan nonon saboda samun damar zuba, dan kofofin su bude.
● ´MOTSA SHA'AWA ●
Man zaitun yana motsa sha'awa in an shafashi lokacin da ake yi wasa.
CIWON SAIFA
duk mutumin da yake ciwan saifa, sai ya hada man zaitun da garin habbatussauda da kuma farar saka ya sha, insha Allah.
ꉂ TSUTSAR CIKI๑σ
duk mutumin da yake da tsutsar ciki, to sai a samu man zaitun da garin habbatussauda da zuma ya kwaba su yasha, wannan tsutsar zata mutu.
=^CIWAN HANJI (ULCER)^=
Duk mutumin da yake da gyanbon ciki, to sai ya samu garin habbatussauda kamar cokali daya sannan ya samu garin (kumasari)da ganyan zaitun mai laushi yaji kasu ya dinga sha har sai ya warke.

ó㉨ò FITSARIN KWANCE ó㉨ò
Duk yaro da yake fitsarin kwance, to sai a samu garin zaitun Dana habbatussauda a zuba a nono a dinga bashi yana sha zai dai na. Insha Allah
∈MUTUWAR JIKI(KASALA)∋
Duk mutumin da jikinsa yake yawan mutuwa to sai ya dauwama yana shan zuma da garin habbatussauda zaiji karfin jikinsa.
. √••••YAWAN ZABBABI•••••√
duk mutumin da yake yawan yin zazzabi , to saiya samu garin habbatussauda kamar cikin ludayi ya kwaba da ruwan zafi, da kuma zuma maras hadi ya dinga sha insha Allah
★CUWON GABOBI ★
Duk mutumin da gabobinsa suke ciwo to saiya samu garin habbatussauda da zuma ya dinga sha, sannan kuma ya zuba garin habbatussauda a cikin man zaitun ya dinga shafawa a GABOBI.
∩KWARKWATA∩
duk matar da take fama da kwarkwata kuma har take son rabuwa da ita, to ta samu man zaitun da garin habbatussauda ta kwaba sannan sai ta Bari sai Rana ta take sai ta zubar wannan man a kannata ta barshi yayi kamar minti (20) sannan sai ta wanke insha Allah zata ban kwana da kwarkwata.
◉CIWAN TARI◉
duk mutumin da ya kamu da kowanne irin Tari to sai ya samu garin habbatussauda da man zaitun da yar'citta da tsamiya da zuma, sai ya hadasu guri daya ya cakuda ya dinga ci insha Allah.
/✪ MAJINAR KIRJI ✪\
duk mutumin da yake yawan majinar kirji to sai ya samu man zaitun da garin habbatussauda ya hada ya dinga ci kullum sau biyu (2) safe da yamma.
^▽^TARIN FUKA^▽^
Duk Wanda yake tarin huka to sai ya dinga shan man zaitun cokali daya kullum.

Daga taskar
Dr kabeer ishaq gidan magani
08096343188,
08165351087,

WAKEN SOYA DA AMFANINSA

WAKEN SOYA (SOYA BEANS)

Amfanin waken Soya:
1-Gina jiki.
2-Ciwon suga.
3-Yawan kitse (Cholesterol)
4-Lafiyar qashi.
5-Ciwon daji = "Malignant disease".
5-Kare zuciya da qoda daga illar ciwon suga (Prevent heart & kidney)
6-Ciwon dajin mama (Cancer).
7-Inganta farkuwar jiki.
8-Basir.
9-Matan da suka daina al'ada.
10-Hawan jini (Hypertension).
11-Ciwon zuciya (Heart beat disease)
1-GINA JIKI:
Waken soya yana da sinadari maigina jiki wato "Protein" Wannan sinadari yana da kyau kamar nama amma bashi da maiqo kamar nama. Bashi da "Cholesterol" manya da yara da mata masu ciki da masu cutar qanjamau su yawaita cin waken Soya, ana kuma iya zuba cokalin na garin zogale a madarar waken soya kofi xaya a sha.
2-YAWAN KITSE:
Wannan kitse yayi yawa a jininsa ya yawaita amfani da waken suya saboda yana da "Omega-3- fatty acide" mai rage yawan kitse a jini. Ana so mai yawan kitse ya yawaita amfani da waken soya dafaffe.
3-LAFIYAR QASHI:
Akwai sinadarin "Calcium" a waken soya mai gina qashi da haqora, shi yasa ake baiwa yara masara mai launin rawaya domin tana da wannan sinadari.
4-CIWON DAJI:
Haka kuma waken soya yana taimakawa wajen rage hatsarin kamuwa da cutar ciwon dajin mama (Cancer) da hanji da Prostate masu cutar ciwon daji da masu son yin rigakafin kamuwa da cutar za su iya yawaita amfani da waken soya.
5-KARE ZUCIYA DA QODA:
Masu ciwon suga suna da hatsarin kamuwa da ciwon qoda da ciwon zuciya. masana sun gano cewa waken soya na da abubuwan da suke taimakawa wajen kare zuciya da qodar mai ciwon suga, mai wannan cuta ya yawaita amfani da waken soya.
6-INGANTA GARKUWAR JIKI:
A cikin waken soya akwai sinadarin: Magnesium, manganese, Copper, Selenium da Vitamin B6, shi yasa yake taimako wajen inganta garkuwar jiki. masu cutar qanjamau suma suna da qarancin "selenium" mai son inganta garkuwar jikinsa da na iyalinsa; su yawaita cin waken soya.
6-BASIR (PILE)
Waken soya na da "Dietery fibre" mai rigakafi da kuma maganin Basir mai cutar Basir ya yawaita cin waken soya amma dafaffe don yafi soyayye.
7-MATAN DA SUKA DAINA AL'ADA:
Matan da suka daina al'ada saboda tsufa su yawaita cin waken soya zai taimaka wajen rage musu matsalolin dake zuwa da wannan larurar

Dr kabeer ishaq
08096343188.

Thursday, 26 July 2018

CUTUTTUKAN DASUKE KAMA AL-;AURAR MATA DA MAZA

CUTUTTUKAN DA SUKE DAMUN AL'AURAR MATA, DA MAZA,  WATO (VAGINA DISEASE)

08096343188

Kamar yadda bincike ya nuna cewa akwai cututtuka da yawa masu damun al'aurar 'ya'ya mata, kama daga balagarsu zuwa fara Daukar ciki har zuwa daina al'adarsu. Kamar:
(1)Warin gaba (odour):- Warin gaba na 'ya'ya mata yana samuwa saboda wasu dalilai da suke jawo shi kamar haka:
1- Tafiya ba wando.
2- qin wanke farji bayan jima'i.
3-qin wanke farji da ganyen magarya da misali bayan an yi al'ada.
4-barin wando ya kai kwana uku a jiki.
5-kama ruwa da ruwa mai sanyi qarara.
6-Qin wanke gaba bayan an tsuguna a Masai.
7-Mace ta ringa biyawa kanta buqata da hannu ko wani abu.
Ki sani cewa wari yana fitowa daga gurare uku kamar haka:-
Hammata.
Farji.
Baki.
Saboda haka lallai ne ki bada kulawa ta musamman a wannan gurare.

MUNA GABATAR MUKU DA MASHAHURN MAGUNGUNA
       DAGA KAMFANIN
GIDAN MAGANI HARBAL MEDICINE

1- Cututtukan sanyi,
RIGA KAFINSA YAFI SAUKI A KAN MAGANINSA

Data cikin maganin olsa
    Ka riqa shan Zuma  Cokali 3-4 Bayan Asuba, Da Bayan La'asar Taswon Sati 6
-Yana maganin Hawan Jini kamar haka: a-Ciwon kai, b-Kasa barci, c-Jiri.
         A Hada Da Shan Ruwan Zobo, Da kuma Zogale
      

FA'IDA;
Mace mai son kar miji yaji wari a gareta yayin saduwa sai ta nemi:
a)Miski.
b)Ambar
c)Ganyen magarya
d)Rihatul Hubbi.
e)Zam-zam.
f)Ma'ul – miyahi
Ki haxasu guri xaya ki tafasa kaxan in ya huce ki zuba a buta ki qar ruwa dashi kuma ki shafe gefen farjinki da cinyoyinki da qirjinki to zaki mamaki yadda mijinki zai riqeqi da kyau da nuna soyayya a gareki.
     1- KI LURA DOMIN KAR KI RIKA SA WASU SINADARE A CIKIN GABANKI DOMIN YIN HAKAN NA KAWO CUTAR SANYI
     2-KUMA ANNABI SAW YA HANA MATA SU SA TURARE SU FITA DAGA GIDA

KUMBURIN GABA (INFLAMMATORY)
Qaiqayin gaba da (Pruritis), wannan cututtuka suma suna damun al'aurar 'ya'ya mata qwarai da gaske mai wannan larura ta nemi wadannan abubuwa:
QAIQAYIN FARJI (pruritis)
Kashin akuya.
Tafarnuwa.
Garin hulba.
Man shanu.
Sai ta tafasasu ta dinga shiga ciki da xuminsa sau uku a rana zata warke insha Allah.

ZAFIN GABA (Pain)
Mai fama da wannan matsala sai ta nemi:
Ganyen kabewa.
Ganyen zogale.
Man kaxanya
Majigi.
Hulba.
Sai a hada su guri guda a kwava da man ta ringa shafawa sau uku a rana, duk shafawa sai ta wanke da ruwan xumi za tayi mamaki qwarai.

ZUBAR RUWA (Leaking)
Mai zubar da ruwa a gabanta sai ta samu:-
Saiwar zogale.
Saiwar rai Bore.
Garin tafarnuwa.
A dakesu ayi yaji ta rika amfani dashi    
    FADAKARAWA :-Masu Olsa Hakan Zai Iya Taimaka musu
.
RASHIN HAIHUWA (INFERTILITY)
Wannan ma matsalace wadda take samuwa daga wadannan abubuwa:-
SANYI KO ZAFIN MAHAIFA:
Waxannan suma suna hana mace ta samu ciki saboda illolin, da suke tattare da hakan
08096343188, 08165351087,

(CUTUTTUKAN DA SUKE HANA HAIHUWA) don samun bayani sosai akan "zafi ko sanyin mahaifa).

NAMIJIN DARE:
Wani aljani ne wanda yake aurar 'ya mace kuma ya hanata samun cikin da zata haifar. Alamominsa sune:-
Mafarkin jarirai.
Mafarkin wani na saduwa dake.
Vacin rai da faduwar gaba.
Mafarkin ruwa.
Yawana ciwon kai.
Jin motsi a ciki.
Lalacewar maganar aure ga budurwa.
Damuwa da rama ko qiba marar misali.
MAGANI:
1-KI RIQA KARATUN SURATL BAQARA A CIKIN GIDAN KI,KO KUMA SHI MAI GIDAN YA RIQA YI
2- YAWAN KARANTA AYATUL KURSIYY YAKAN HALLAKA ALJANI
3 -DA SAURAN MAGUNGUNA NA ISLAMIC WANDA BASU KAUCEWA SHARI'A BA

QARIN BAYANI: MATA:-
Akwai cututtuka da yawa da suke samun al'aurar mata saboda bata rabuwa da danshi wanda ta nan ne wasu kwayoyin halitta suke samun zama a cikin al'aurar tasu ana kiransu (Micro – organism) da turanci.
Kusan cewa shi farji da ake magana akan cututtukansa shine wanda Allah ya halitta da wani sinadari na mayen qarfe da wata tsoka kuma tana da baki guda biyu hagu da dama. yayin da sha'awar mace ta motsa sai ta riqa motsi dai-dai kuma tana iya yin rauni ita wannan tsokar har ta daina motsi. Wannan tsoka kamar fulogine a jikin mace yayin da dauxa tayi mata yawa sai ta kasa motsi. A daga nan sai sha'awar 'ya mace ta xauke domin ita wannan tsoka itace ke feso wani ruwa wanda shike sauko da wani ruwa da yake dadada jin dadin mu'amalar jima'i kuma yake sa wani zaqi tsakanin mace da miji. Kuma wannan motsi da yake naman akwai wani sinadarin kitse wanda Allah yasa akan saman kaciyarsa da namiji idan sha'awarsa tai motsei sai kaji yana motsi dai-dai, lokacin da namiji ya kawo zata ji yana wannan motsi kuma shima namiji yana iya jin motsin na mace yayin da ta rigashi inzali ko kawowa. Wadannan motsi guda biyu su ake cewa: jauharatul jima'i idan na daya daga ma'aurata ya sami matsala sai kaga auren yaqi zaman lafiya. Amma idan ba matsala sai kaga ana zaune lafiya cikin shauqi da annashuwa.

ALAMONIN CUTUKAN AL'AURAR MACE
Alamomin masu nuni izuwa kamuwar cutar al'aurar mace ya danganta da irin ciwon da abin da ya jawoshi. Kadan daga ciki:-
1-Zafi yayin fitsari. (burning during urinate).
2-Ciwo daga wajen a'aurarta (Itching out side the vagina).
3-Canzawar gaba ba kamar yadda ta saba ganiba.
4-Zafi yayin saduwa da miji (discomfort during sexual intercourse).
Qaiqayi da ake kira da (Irritation).

MAZA:-
Kamar yadda muka taba Bangaren mata yana da kyau mu taba bangaren maza kamar haka:-
Farko suma maza suna da cututtuka da suka kama al'aurarsu. 

HALITTARSA  
1-Wannan wata ma'aikata ce da Allah ya ginatakuma ya samar da ita don wanzar da samuwar dan adam da kuma fitar da Wasu Batattun abinchi da cutuka daga jikin Da Namiji   
2-Ku sani akwai manyan jijiyoyi guda hudu a jikin azzakarin kowane da namiji,daya ta jinin daya gama aiki, daya ta jinin Da zai kai Abinci zuwa ga kwayoyi da ke jikinsa, daya kuma ta maniyyi,Ta karshe itace wadda ke kai sako zuwa kwakwalwa sannan ta dauko sakon daga kwlkwalwa zuwa Ita Halittar Da Namiji
  3-Waxannan jijiyoyi suna kama da bututu kuma suna rufe ne amma ba gaba daya ba,
    4- Duk lokacin Da sha'awa tazowa Namiji sai jijiyar sako ta kai kwakwalwa,wata kuma ta dauko sakon daga can zuwa Gaban Namiji,Sai Jini Ya qaro zuwa Gaban Namiji Sai Al'aurar ta kumbura.  
ALAMOMIN CUTUTTUKAN AL'AURAR
alamomu sun hada da:
,Zafin qirji (chest pain),
Juyawar ciki (stomach upset).
- Karancin Ruwan Maniyyi
Rashin Karfin Gaba
-Saurin Inzali
-Karancin Sha'awa
Kasa Saduwa da Iyali  -Raunin Gaba
    DUK MATSALOLIN DA ZASU TABA HANYOYIN NAN GUDA HUDU SUNE SUKE KAWO ILLA GA AL'AURAR MAZA, WATO:          HANYAR JINI          SAKO ZUWA /DAGA KWAKWALWA          SINADARAN DAKE QARA SHA'AWA ACIKIN JINI.

CUTUTTUKAN MA'AURATA:
Qari akan cutuka dake damun ma'aurata sun hada da:-
1-DAMSU SHA'AWAH :
Wannan wata cutace da basir yake kawota musamman ga ma'aurata, alamarta shine; xaukewar sha'awa da ni'imar mace qaiqayin gaba da sa faxuwar gaba, zubewar nono gaba xaya. shiko namiji raunin jijiyoyin azzakari rashin qarfi da rashin gamsar da iyali, in yayi ma ba zai iya komawaba.
2-SANYIN MATA:
Alamarsa shine; fitar farin ruwa ta gaba, rashin sha'awa, ciwon mara, qurajen farji da qaiqayi.
3-YANKAN GASHI:
Alamar xauke jin daxi yayin saduwa jin zafi yayin saduwa, tsikewar gaba inya daxe yakan iya zama faso.
4-BAKIN SANYI :
Alamarsa shine; jin qaiqayi a jiki, jin motsin ciki, kamar kina da ciki, ciwon mara in yayi nisa yana iya hana haihuwa.
5-ZAFIN MAHAIFA:
Idan yai yawa yana ruvar da maniyyin daya shiga cikin mahaifa wanda sanadiyar haka ciki ba zai samu ba.
6-SANYIN MAHAIFA:
Idan sanyi yaiwa mahaifa yawa to in maniyyi ya shiga sai sanyin yai masa yawa dalilin haka sai maniyyi yaMutu saboda sanyin yayi masa yawa

ALAMUN RASHIN HAIHUWA NA BANGAREN SANYI SUNE:
Fitar farin ruwa ta gaba.
Qaiqayin jiki da na farji.
Yawon wani abu kamar tana.
Ciwon qirji, baya, zafin jiki da sauransu.
MAGANI:
A nemo saiwar zogale guda
Tafarnuwa guda a hada da garin hano a tafasa ta dinga shan kofi xaya sau uku a rana. sannan ta dinga yawan shan kwallon tafarnuwa da ma'ul-miyahi sau uku a kullum zata samu ciki a cikin wata uku , 

Daga
Gidan magani

Friday, 13 July 2018

MAGANIN GARGAJIYA AKASAR HAUSA KASHI NA 4

MAGANIN
            GARGAJIYA
        A KASAR HAUSA 
             KASHI NA 4

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
Gidan magani
08096343188, 08165351088,
mkabeer5618@gmail.com

Kashi na (4)
MATSAYIN MAGANI
maganin gargajiya na hausawa yanada babban matsayi a al'adar hausawa domin kuwa shine maganin da hausawa suka gada tun iyaye da kakanni,  kafin shigowar turawa kasar hausa dama bayan shigowar su ana amfatani da yayan itatuwa da sakesaki  da sauyoyi da ganyayen itatuwa da tsirrai kala daban daban domin magance cututtuka  haka ma hausawa suna amfani da wasu abubuwa daban kamar sassan jikin dabbobi da kwari da tsuntsaye domin magance cututtuka  wani lokacin ma harda wajen hada sihirce sihirce,  
Sabida yadda hausawa suka yadda da irin wadannan magunguna yasa duk da cewa turawa sunkawo magunguna amma hausawa basu daina amfani da maganin gargajiya ba harma wani lokacin in akayi magani a asibiti akaga ya gagara saikaji ance wannan ba na asibiti bane nagida za'ayi wato na gargajiya, 

Tafuskar addinin musulinci maganin gargajiya yanada mtukar amfani domin kuwa annabi muhammad (s.a.w) yayi horo ga musulmi surika amfani da yayan itatuwa ganyaye da sauransu domin kuwa akwai amfani acikinsu, 
Awani hadisinma cewa yayi  INA HORONKU DA KITIKI WANNAN ITACIYA TA HINDU DOMIN ACIKINTA AKWAI WARAKA BAKWAI (7)

an bayyana itaciyar hindu  tana kama da giginya,   
Kumaanzon alllah s.a.w yace haramunne ga musulmi yayi amfani da najasa ko wani surkulle wajen maganin kowacce irin cuta.
Alhamdu lillah  yanzu kuma zamu fara bayanin wasu daga cikin magunguna na gargajiya tun daga na hausawa  har ma da na wasu yarurrukar da iznin allah

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
Gidan magani
08096343188, 08165351087,
mkabeer5618@gmail.com

Ayanzu zamu fara da
MAGUNGUNAN JARIRAI DA KANANAN YARA

akwai cututtuka wanda sukafi kama jarirai da yara kanana  abin nufi anan shine ireiren wadannan cututtuka suhada da sanyin ciki,  da ciwon saifa,   ciwon kai,   da kazamin goyo,  da ciwon balli balli,  da ciwon damsai,  da ciwon tamalmala,   da ciwon ela,  dadai sauransu
Gasu kamar haka

MAGANIN SANYIN CIKI
ciwon sanyin ciki ciwone dayake matukar takurawa jarirai da yara kanan har sukai kamar shekara 10 da haihuwa
Wannan ciwo yakan samo asali ne tudaga sanda yaro yake cikin cikin mahaifiyarsa,  awannan lokaci in ciki yasoma girma sai mai cikin tarika fuskantar yawan jin zafi ajikinta wanda hakan yakan tilastata tarika yawan kwanciya waje mai sanyi,  shan abubuwa masu sanyi,  wannan sanyi shine yake shafar jarirai  hakama in ana kwantar da jariri awaje mai danshi shima zai iya sawa sanyi yakamashi

Yadda ake gane jariri yakamu da sanyi
# yawan tari ko atishawa
# yawan citar da majina ko toshewar hanci
# yawan amai mai kama da danyen kwai
INHAKA TAFARU GA MAGANI
Asamu saiwar DASHI da saiwar FIDDA TARTSA da saiwar KAYAR BERA ahadasu ayayyanka azuba a tukunya tare da farar kanwa da curi daya na manshanu adafa saiya tafasa sosai sannnan asauke inya huce arika bawa jariri yanasha safe da yamma idan kuma yaron yana shan nono itama mahaifiyar yaron sai tarika sha safe da yamma itama zaimata amfani a cikinta, 
 
Muhadu a darasi na gaba insha allah zamuci gaba da bayanan magungunan jarirai da sauran magunguna 

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
Gidan magani
08096343188, 08165351087,
mkabeer5618@gmail.com

Friday, 6 July 2018

MAGANIN GARGAJIYA A KASAR HAUSA KASHI NA 3

MAGANIN
                GARGAJIYA
         A KASAR HAUSA (3)

                Daga taskar
              Dr kabeer ishaq
               Gidan magani
               08096343188
       Kashi na uku (3)
Assalamu alaikum wa rahmatullah kamar yadda muka yi bayani a darasi na 2 akan tatihin maganin gargajiya a kasar hausa   inshaa allah yanzu zamu dora bayani akan

ASALIN DABARAR YIN MAGANI A KASAR HAUSA 
Idan muka koma kan asalin hanyar da dan adam yasamu dabarar yin magani dan warkar da cuta dakuma kare kai daga kamuwa daga cututtuka,  shima akwai hasashe daban daban da masana ilmin magunguna suka kawo,

Hanya tafarko da aka bayyana amatsaayin  wadda dan adam yasami wannan hikima itace ta jarraba abubuwa da allah ya yalwata a kusa dashi, 
An kara bayyana cewa akwai itatuwa da tsirrai da sinadarai a ko ina kuma a yalwace a cikin wannan duniya tamu,   wanda tahanyar gwadasu ne a lokacinda dan adam yasamu wata matsala ta rashin lafiya akesamun hanyar warkar da  cututtuka iri daban daban,
Masu irin wannan ra'ayi suna ganin tawannan hanyar ne magani yasamu asali har yakai matsayin da yake ayanzu,

Hasashe na 2ya bayyana cewa magani yasamo asali daga tsuntsaye da dabbobi da kwari na gida dana daji awannan raaryi anaganin magani yasamo asali ne da irin tsirrai wanda tsuntsaye da dabbobi suke ci, ,  wai tahaka ne halittu suke samun lafiya sabida akwai nau'in abinci dasukeci in sunada lafiya kuma akwai wanda sukeci in basuda lafiya,  masu wannan ra'ayi sunce tahaka ne dan adam yagane ire iren hakukuwan da idan akayi amfani dasu za'a iya samun waraka.

Wani hasashen kuma ya bayyana cewa magani dai yasamo asali ne a sakamakon baiwar da allah yayiwa dan adam ta sanin cutuka da magunguna,  masu irin wannanra'ayin suna ganin mutane suna samun wannan baiwa ne a lokacin da wani ciwo yakamasu,   
    Idan muka nazarci wannan hasashe na salin magani zamuga cewa ra'ayi na uku yafi daukar hankali dan kuwa tunfarko anbayyana cewa allah shine ya halicci mutum kuma yahalicci cuta da magunguna daban daban amma fa waraka a hannunsa take.

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
08096343188

(BUNKASAR MAGANI)
a sakamakon barnar da cuta takeyiwa dan adam kuma da son nuna bajinta da neman daukaka yasashi fafutika dan neman ire iren magungunan da zasu taimaka masa ko yayi rigakafi ko magance cututtuka  dan haka wannan daliline yakawo samuwar irin wannan mutane acikin al'ummar hausawa,   shiyasa ma wasu suka dauki bada magani amatsayin gadon gidansu na iyaye da kakannin
dan haka hausawa masu bada magani sun kasu kashi 2 akwai wanda suka gada akwai wanda basu gada ba.

(MASU MAGANIN GADO)
Masu bada maganin gargajiya wanda suka gada sun gada ne awajen iyayensu da kakanninsu dan haka irin wannan mutane sunhada da masu sana'o'i na gargajiya     musali
*MAKERA
suna bada maganin kunan wuta dakuma tsatsube tsatsube dasuka danganci wannan sana'a kamar wasa da wuta da makamantansu
*MASUNTA
suna bada maganin sarkewar kayarkifi a makogwaro da maganin sanyin jiki dana iskokan ruwa dakuma wannan sana'a.
*MANOMA
suna bada maganin ciwon baya dana karfin jiki da juriya dakuma tsatsube tsatsube na noma.
*MAHAUTA
suna bada maganin jini da sarkewar nama ko kashi a makogwaro suma sunada nasu tsatsube tsatsuben.
*MAHARBA
suna bada maganin iskokai dana mayu dana fargaba dana dafi da kaudabara da maganin bindiga dadai sauransu.
*MASAKA
Suna bada maganin basur
*FATAKE
suna bada maganin daurin daji da maganin barayi.
*MADORA
suna bada maganin karaya da targade da amosanin kashi da makamantansa.
*WANZAMAI
suna bada maganin jini dana mayu da cututtuka iri daban daban wadanda suka shafi jikin jarirai dana yara kanana damanya maza da mata haka kuma suna bada magunguna dasuka shafi tsatsube tsatsube da surkulle kalakala.
*AKWAI WASU KUMA
akwai wasu mutane dasuka gaji bayarda maganin gargajiya kamar yar mai ganye da dan magori dakuma wasu wanda suka nakalci bada maganin wasu cututtuka wanda zakuji wani lokacin anacewa ai maganin matsala kaza sai gidan wane.

WANDA BASU GAJI BADA MAGANI BA
Irin wannan mutane suna samun wannan hikima wasu insunyi rashin lafiya kuma sukayi amfani dawani magani suka saku biyan bukata daga wannan lokacin in sukaji wanda yakeda irin wannan lalurar saikaga subashi wasu kuma kawai insunji anfada shikenan sun rike sai surika bayarwa  ireiren wannan Mutane sunhada da BOKAYE DA UNGUWAR ZOMA DA SAURANSU  wasu kuma suna samun maganinsu tahayar wani masanin maganin in ya nakalta masu asalaintushen maganin...

Zan dakata anan muhadu a darasi na gaba
Zakiji bayani akan matsayin magani harma da wasu daga cikin magunguna in shaa allah

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
Gidan magani harbal medidine center
08096343188, 08165351087,
mkabeer5618@gmail.com

Friday, 8 June 2018

MAGANIN GARGAJIYA A KASAR HAUSA kashi na 2

MAGANIN
         GARGAJIYA
     A KASAR HAUSA (2)

         DAGA TASKAR
       DR KABEER ISHAQ   
         GiDAN MAGANI
08096343188,08165351087

assalamu alaikum wa  rahmatullah 
In ba,a manta ba a darasi nafarko munyi bayani akan tarihin maganin gargajiya a kasar Hausa

Yau kuma zamu tabo bayani akan

ASALIN MAGANI DA NA'ANAR CUTA
shidai MAGANI ko hanyar  warkar da cuta baza'a ce  ga lokacinda aka farashi a duniya ba wannan daliline yasa kowacce al'umma takeda nata  kalar hanyoyin wajen bada MAGANI  saboda haka kafin  MU tsunduma cikin wannan nazari  yanada  kyau musan irin  fassarar da hausawa suka bawa MAGANI

Haka kuma asani cewa ba'a iya raba MAGANI da cuts Dan kuwa suna tafiya ne  kafada da kafada da juna daya  bayayin tasiri Sai da dayan,  dan kuwa ansani cewa badan samuwar cuta ba da Dan Adam baisan MAGANI ba haka kuma badan amfanin MAGANI ba da Dan Adam baici mutuncin cuta ba ,
Dan haka Sai mu fahinci MAGANI yana matukar taka rawa awajen hausawa

👍MA'ANAR CUTA👍🏼
A hakika masana da dalibai masu nazari akan al'adun hausawa  sunyi faman kaiwa da komowa wajen fassara Kalmar cuta,
Dangane da wannan nazari ga kadan daga cikin ire iren wannan fassarori,

Cuta na nufin Shiga wani yanayi na rashin jin dadin jiki ko halin da kansa  damuwa ga mairai ko wani bangare na jiki yasamu rauni ko nakasa  ko hankali yatabu Wanda wani lokaci irin  wannan yanayi ko hali in anshiga yakanyi sanadiyyar mutum yarasa ransa,

Dr Kabeer ishaq
gidan maganin
08096343188

🌷MA'ANAR MAGANI🌷
Kalmar MAGANI  Hausa CE tantagaryar Hausa wacce babu wani kancilko ko shishshigin aro a kirkirar ta da furucin ta a fagen nazari  masana da manazarta sunkawo ra'ayoyi dayawa mabambanta dangane da MA'ANAR wannan kalma
Fassara  ta 1
1) MAGANI wata hanya ce taneman biyan bukata akan wata matsala dake damun mutum ko wacce take yiwa rayuwarsa barazana,
Dan haka wannan fassarar tana nuna  ba'a bukatar MAGANI Sai alokacin da wata matsala tataso  anan  an manta da fannonin magungunan surkulle da makamantansu,

Fassara  ta 2
2) MAGANI shine duk wani Abu Dan. Adam zaiyi Dan samun waraka da kuma bukatu na rayuwa,  Dan kuwa Dan Adam kullum fafutika yake  wajen Neman maganin cutuka da kwantar da damuwar zuciya da daukaka da kariya Dan haka shi mutum kullum yana cikin Neman MAGANI inya gama wanchan to Sai yashiga Neman wancan.....
Bakin gwargwado wannan manazarci yafito da ma'ana a bangarorin maganin gargajiya na hausawa,

Fassara ta 3
3) MAGANI shine duk wani Abu kowata hanya da akebi domin gusar da cuta daga jikin mutum kokuma kwantar da ita  Dan Kawo jindadi ga jiki ko ga zuciya ko saukaka damuwa wadda cutar take haifarwa 
Shikuma wannan manazarcin yamanta da iron magungunan da hausawa sukeyi Dan cutar da wash mutane ko nuns bajinta awaken wasannin gargajiya da makamantansu 

Fassara  ta4
4) MAGANI yana nufin kokarin kawar da cuta ko wacce iri ko kwantar da it's kokuma Neman kariya saga kamuwa da cuta ko abokan hamayya kokuma nuns bajinta tahanyoyi daban daban

Akwai fassarori dayawa da masu nazari sukayi akan MAGANI da cuta

Amma zan takaita anan  Sai a darasi nagaba zamu Dora bayani akan asalin dabarar yin MAGANI akasar Hausa

Saga taskar
Dr Kabeer ishaq
gidan maganin
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com
www.gidanmagani.blogspot.com
ko a tuntubemu a shafinmu na Facebook

gidan maganin gargajiya (traditional medicine)

Sunday, 27 May 2018

CUTA DA MAGANIN GARGAJIYA A KASAR HAUSA

CUTA DA MAGANIN
       GARGAJIYA
   A KASAR HAUSA. (1)

    DAGA TASKAR
    DR KABEER ISHAQ
         GIDANMAGANI
08096343188,08165351087

Assalamu alaikum Wa rahmatullah  Fatan alkhairi ga dukkan masu bibiyar shafukan mu na magunguna a internet  Tareda sauran Al'uma gabaki daya
Bayan haka in shaa Allah ayau zamu Fara gabatar da wannan darasi maifadi wanda aka sawa suna 🌷CUTA DA MAGANIN GARGAJIYA A KASAR HAUSA🌷 wanda saidai muyi gwargwadon Hali sabida dadin darasin    wanda dayawa daga cikin darussan an cirosu daga cikin manyan littattafai na manyanyan malamai dasukayi akan magunguna  Allah yabamu ikon amfana da abinda yake cikin wannan darussan  ameen thumma Ameen

======================
Asakamakon binciken da masana da manazarta  akan al'adu da kuma malaman addini suka gabatar sun baiyana cewa gabanin halittar duk wata halittar duniya Allah ya halicci Magani, wadannan masana sun Kara da cewa Allah shine mai warkarwa maganin da ake sarrafawa sanadi ne kawai,   kuma malaman addinin musulunci  sunce Annabi musa (A. S) ya tambayi Allah maigirma da daukaka cewa
    "wayakawo cuta "?
"allah yace nine "
"yace wayake warkarwa"?
"yasake amsawa dacewa nine "
"daga nan sai yace menene aikin masu magani"?
Sai Allah yace cika umarninmu suke " 

Dan haka idan muka nazarci wannan tambayoyi da amsoshi zamu iya cewa Allah yaba Kowacce Al'uma dake cikin wannan duniya halittun itace da tsirrai a doron kasa wanda zasu rika diba su sarrafa ta hanyoyi mabambanta domin yin maganin cututtukan da suke damunsu,

Dan haka acikin kasa Akwai albarkatu masu dimbin yawa wanda daga cikinsu akasanya WARAKA ga Cututtuka dakuma bukatocin halittun dake bayan kasa haka kuma a tsakiyar sararin duniya aka SANYA iska da haske na yanayi daban daban wanda suke fasalta shekara wanda daga cikinsu ne ake samun cutuka da WARAKAr halittun dasuke cunkushe acikin wannan duniya,

Saboda haka zamu iya cewa ita Kanta wannan duniya Allah ya tsarata daidai da yadda za'a samu kiwon lafiyar halittun da suke rayuwa acikinta,
Danhaka babu wata Al'uma acikin duniya da bata amfani da Magani  haka kuma babu wani lungu da sako a duniya da za'ace cuta bata ziyarci wajen ba,

Abinda za'a iya cewa shine hanyoyin diban Magani da sarrafashi sun bambanta kamar yadda ire iren cutuka suka da hanyoyin kasuwa dasu suka bambanta-

Dan shawara ko Karin bayani
Atuntubi GIDANMAGANI
"08096343188"

+Abisa La'akari da wannan bayanai da suka gabata zamu iya cewa dukkan halittun dasuke rayuwa a bayan kasa na kowanne irin jinsi  suna tattare da abubuwa "uku " wato
+cuta ko ciwo
+lafiya.
+Magani
Anyi ittifaki cewar acikinsu Magani akafara samu sannan cuta sai lafiya tabiyo baya,

Dan haka Kowacce halitta lokacin da takamu da wata rashin lafiya sai tabazama neman maganin da zai taimaka Asamu WARAKA daga wannan cuta domin lafiya yasamu wajen zama wannan yakara baiyana mana cewa Magani yariga cuta samuwa. Shiyasa da kamu da cuta sai atafi neman maganinta,

Wannan daliline yasa wararen da cuta bata Kama ba ake tanadin Riga kafi Dan Kar cutar tazo wajen,
Allah maigirma da daukaka yasanar da wasu daga cikin bayinsa  makaloli da ilmin sanin amfanin wasu itatuwan da tsirrai da dai sauransu kamar yadda zamuji a darasi nagaba in Allah yayarda.

Daga taskar
Dr Kabeer ishaq
Gidanmagani
08096343188.08165351087
mkabeer5618@gmail.com
www.gidanmagani.blogspot.com