MAGANIN
GARGAJIYA
A KASAR HAUSA (2)
DAGA TASKAR
DR KABEER ISHAQ
GiDAN MAGANI
08096343188,08165351087
assalamu alaikum wa rahmatullah
In ba,a manta ba a darasi nafarko munyi bayani akan tarihin maganin gargajiya a kasar Hausa
Yau kuma zamu tabo bayani akan
ASALIN MAGANI DA NA'ANAR CUTA
shidai MAGANI ko hanyar warkar da cuta baza'a ce ga lokacinda aka farashi a duniya ba wannan daliline yasa kowacce al'umma takeda nata kalar hanyoyin wajen bada MAGANI saboda haka kafin MU tsunduma cikin wannan nazari yanada kyau musan irin fassarar da hausawa suka bawa MAGANI
Haka kuma asani cewa ba'a iya raba MAGANI da cuts Dan kuwa suna tafiya ne kafada da kafada da juna daya bayayin tasiri Sai da dayan, dan kuwa ansani cewa badan samuwar cuta ba da Dan Adam baisan MAGANI ba haka kuma badan amfanin MAGANI ba da Dan Adam baici mutuncin cuta ba ,
Dan haka Sai mu fahinci MAGANI yana matukar taka rawa awajen hausawa
👍MA'ANAR CUTA👍🏼
A hakika masana da dalibai masu nazari akan al'adun hausawa sunyi faman kaiwa da komowa wajen fassara Kalmar cuta,
Dangane da wannan nazari ga kadan daga cikin ire iren wannan fassarori,
Cuta na nufin Shiga wani yanayi na rashin jin dadin jiki ko halin da kansa damuwa ga mairai ko wani bangare na jiki yasamu rauni ko nakasa ko hankali yatabu Wanda wani lokaci irin wannan yanayi ko hali in anshiga yakanyi sanadiyyar mutum yarasa ransa,
Dr Kabeer ishaq
gidan maganin
08096343188
🌷MA'ANAR MAGANI🌷
Kalmar MAGANI Hausa CE tantagaryar Hausa wacce babu wani kancilko ko shishshigin aro a kirkirar ta da furucin ta a fagen nazari masana da manazarta sunkawo ra'ayoyi dayawa mabambanta dangane da MA'ANAR wannan kalma
Fassara ta 1
1) MAGANI wata hanya ce taneman biyan bukata akan wata matsala dake damun mutum ko wacce take yiwa rayuwarsa barazana,
Dan haka wannan fassarar tana nuna ba'a bukatar MAGANI Sai alokacin da wata matsala tataso anan an manta da fannonin magungunan surkulle da makamantansu,
Fassara ta 2
2) MAGANI shine duk wani Abu Dan. Adam zaiyi Dan samun waraka da kuma bukatu na rayuwa, Dan kuwa Dan Adam kullum fafutika yake wajen Neman maganin cutuka da kwantar da damuwar zuciya da daukaka da kariya Dan haka shi mutum kullum yana cikin Neman MAGANI inya gama wanchan to Sai yashiga Neman wancan.....
Bakin gwargwado wannan manazarci yafito da ma'ana a bangarorin maganin gargajiya na hausawa,
Fassara ta 3
3) MAGANI shine duk wani Abu kowata hanya da akebi domin gusar da cuta daga jikin mutum kokuma kwantar da ita Dan Kawo jindadi ga jiki ko ga zuciya ko saukaka damuwa wadda cutar take haifarwa
Shikuma wannan manazarcin yamanta da iron magungunan da hausawa sukeyi Dan cutar da wash mutane ko nuns bajinta awaken wasannin gargajiya da makamantansu
Fassara ta4
4) MAGANI yana nufin kokarin kawar da cuta ko wacce iri ko kwantar da it's kokuma Neman kariya saga kamuwa da cuta ko abokan hamayya kokuma nuns bajinta tahanyoyi daban daban
Akwai fassarori dayawa da masu nazari sukayi akan MAGANI da cuta
Amma zan takaita anan Sai a darasi nagaba zamu Dora bayani akan asalin dabarar yin MAGANI akasar Hausa
Saga taskar
Dr Kabeer ishaq
gidan maganin
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com
www.gidanmagani.blogspot.com
ko a tuntubemu a shafinmu na Facebook
gidan maganin gargajiya (traditional medicine)
No comments:
Post a Comment