Powered By Blogger

Friday, 8 June 2018

MAGANIN GARGAJIYA A KASAR HAUSA kashi na 2

MAGANIN
         GARGAJIYA
     A KASAR HAUSA (2)

         DAGA TASKAR
       DR KABEER ISHAQ   
         GiDAN MAGANI
08096343188,08165351087

assalamu alaikum wa  rahmatullah 
In ba,a manta ba a darasi nafarko munyi bayani akan tarihin maganin gargajiya a kasar Hausa

Yau kuma zamu tabo bayani akan

ASALIN MAGANI DA NA'ANAR CUTA
shidai MAGANI ko hanyar  warkar da cuta baza'a ce  ga lokacinda aka farashi a duniya ba wannan daliline yasa kowacce al'umma takeda nata  kalar hanyoyin wajen bada MAGANI  saboda haka kafin  MU tsunduma cikin wannan nazari  yanada  kyau musan irin  fassarar da hausawa suka bawa MAGANI

Haka kuma asani cewa ba'a iya raba MAGANI da cuts Dan kuwa suna tafiya ne  kafada da kafada da juna daya  bayayin tasiri Sai da dayan,  dan kuwa ansani cewa badan samuwar cuta ba da Dan Adam baisan MAGANI ba haka kuma badan amfanin MAGANI ba da Dan Adam baici mutuncin cuta ba ,
Dan haka Sai mu fahinci MAGANI yana matukar taka rawa awajen hausawa

👍MA'ANAR CUTA👍🏼
A hakika masana da dalibai masu nazari akan al'adun hausawa  sunyi faman kaiwa da komowa wajen fassara Kalmar cuta,
Dangane da wannan nazari ga kadan daga cikin ire iren wannan fassarori,

Cuta na nufin Shiga wani yanayi na rashin jin dadin jiki ko halin da kansa  damuwa ga mairai ko wani bangare na jiki yasamu rauni ko nakasa  ko hankali yatabu Wanda wani lokaci irin  wannan yanayi ko hali in anshiga yakanyi sanadiyyar mutum yarasa ransa,

Dr Kabeer ishaq
gidan maganin
08096343188

🌷MA'ANAR MAGANI🌷
Kalmar MAGANI  Hausa CE tantagaryar Hausa wacce babu wani kancilko ko shishshigin aro a kirkirar ta da furucin ta a fagen nazari  masana da manazarta sunkawo ra'ayoyi dayawa mabambanta dangane da MA'ANAR wannan kalma
Fassara  ta 1
1) MAGANI wata hanya ce taneman biyan bukata akan wata matsala dake damun mutum ko wacce take yiwa rayuwarsa barazana,
Dan haka wannan fassarar tana nuna  ba'a bukatar MAGANI Sai alokacin da wata matsala tataso  anan  an manta da fannonin magungunan surkulle da makamantansu,

Fassara  ta 2
2) MAGANI shine duk wani Abu Dan. Adam zaiyi Dan samun waraka da kuma bukatu na rayuwa,  Dan kuwa Dan Adam kullum fafutika yake  wajen Neman maganin cutuka da kwantar da damuwar zuciya da daukaka da kariya Dan haka shi mutum kullum yana cikin Neman MAGANI inya gama wanchan to Sai yashiga Neman wancan.....
Bakin gwargwado wannan manazarci yafito da ma'ana a bangarorin maganin gargajiya na hausawa,

Fassara ta 3
3) MAGANI shine duk wani Abu kowata hanya da akebi domin gusar da cuta daga jikin mutum kokuma kwantar da ita  Dan Kawo jindadi ga jiki ko ga zuciya ko saukaka damuwa wadda cutar take haifarwa 
Shikuma wannan manazarcin yamanta da iron magungunan da hausawa sukeyi Dan cutar da wash mutane ko nuns bajinta awaken wasannin gargajiya da makamantansu 

Fassara  ta4
4) MAGANI yana nufin kokarin kawar da cuta ko wacce iri ko kwantar da it's kokuma Neman kariya saga kamuwa da cuta ko abokan hamayya kokuma nuns bajinta tahanyoyi daban daban

Akwai fassarori dayawa da masu nazari sukayi akan MAGANI da cuta

Amma zan takaita anan  Sai a darasi nagaba zamu Dora bayani akan asalin dabarar yin MAGANI akasar Hausa

Saga taskar
Dr Kabeer ishaq
gidan maganin
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com
www.gidanmagani.blogspot.com
ko a tuntubemu a shafinmu na Facebook

gidan maganin gargajiya (traditional medicine)

Sunday, 27 May 2018

CUTA DA MAGANIN GARGAJIYA A KASAR HAUSA

CUTA DA MAGANIN
       GARGAJIYA
   A KASAR HAUSA. (1)

    DAGA TASKAR
    DR KABEER ISHAQ
         GIDANMAGANI
08096343188,08165351087

Assalamu alaikum Wa rahmatullah  Fatan alkhairi ga dukkan masu bibiyar shafukan mu na magunguna a internet  Tareda sauran Al'uma gabaki daya
Bayan haka in shaa Allah ayau zamu Fara gabatar da wannan darasi maifadi wanda aka sawa suna 🌷CUTA DA MAGANIN GARGAJIYA A KASAR HAUSA🌷 wanda saidai muyi gwargwadon Hali sabida dadin darasin    wanda dayawa daga cikin darussan an cirosu daga cikin manyan littattafai na manyanyan malamai dasukayi akan magunguna  Allah yabamu ikon amfana da abinda yake cikin wannan darussan  ameen thumma Ameen

======================
Asakamakon binciken da masana da manazarta  akan al'adu da kuma malaman addini suka gabatar sun baiyana cewa gabanin halittar duk wata halittar duniya Allah ya halicci Magani, wadannan masana sun Kara da cewa Allah shine mai warkarwa maganin da ake sarrafawa sanadi ne kawai,   kuma malaman addinin musulunci  sunce Annabi musa (A. S) ya tambayi Allah maigirma da daukaka cewa
    "wayakawo cuta "?
"allah yace nine "
"yace wayake warkarwa"?
"yasake amsawa dacewa nine "
"daga nan sai yace menene aikin masu magani"?
Sai Allah yace cika umarninmu suke " 

Dan haka idan muka nazarci wannan tambayoyi da amsoshi zamu iya cewa Allah yaba Kowacce Al'uma dake cikin wannan duniya halittun itace da tsirrai a doron kasa wanda zasu rika diba su sarrafa ta hanyoyi mabambanta domin yin maganin cututtukan da suke damunsu,

Dan haka acikin kasa Akwai albarkatu masu dimbin yawa wanda daga cikinsu akasanya WARAKA ga Cututtuka dakuma bukatocin halittun dake bayan kasa haka kuma a tsakiyar sararin duniya aka SANYA iska da haske na yanayi daban daban wanda suke fasalta shekara wanda daga cikinsu ne ake samun cutuka da WARAKAr halittun dasuke cunkushe acikin wannan duniya,

Saboda haka zamu iya cewa ita Kanta wannan duniya Allah ya tsarata daidai da yadda za'a samu kiwon lafiyar halittun da suke rayuwa acikinta,
Danhaka babu wata Al'uma acikin duniya da bata amfani da Magani  haka kuma babu wani lungu da sako a duniya da za'ace cuta bata ziyarci wajen ba,

Abinda za'a iya cewa shine hanyoyin diban Magani da sarrafashi sun bambanta kamar yadda ire iren cutuka suka da hanyoyin kasuwa dasu suka bambanta-

Dan shawara ko Karin bayani
Atuntubi GIDANMAGANI
"08096343188"

+Abisa La'akari da wannan bayanai da suka gabata zamu iya cewa dukkan halittun dasuke rayuwa a bayan kasa na kowanne irin jinsi  suna tattare da abubuwa "uku " wato
+cuta ko ciwo
+lafiya.
+Magani
Anyi ittifaki cewar acikinsu Magani akafara samu sannan cuta sai lafiya tabiyo baya,

Dan haka Kowacce halitta lokacin da takamu da wata rashin lafiya sai tabazama neman maganin da zai taimaka Asamu WARAKA daga wannan cuta domin lafiya yasamu wajen zama wannan yakara baiyana mana cewa Magani yariga cuta samuwa. Shiyasa da kamu da cuta sai atafi neman maganinta,

Wannan daliline yasa wararen da cuta bata Kama ba ake tanadin Riga kafi Dan Kar cutar tazo wajen,
Allah maigirma da daukaka yasanar da wasu daga cikin bayinsa  makaloli da ilmin sanin amfanin wasu itatuwan da tsirrai da dai sauransu kamar yadda zamuji a darasi nagaba in Allah yayarda.

Daga taskar
Dr Kabeer ishaq
Gidanmagani
08096343188.08165351087
mkabeer5618@gmail.com
www.gidanmagani.blogspot.com

Friday, 20 April 2018

AMFANIN NAMIJIN GORO

ko kunsan amfanin namijin goro ajikin mutum ????
======================

Namijin goro wanda a ka fi sani da 'garcinia kola' yawanci a fi samunsa a kasashen Afirka, kuma shekaru aru-aru a na amfani da shi don yin magani a al'adun Afirka, don sai ku gyara zama ku karanta fa’idar amfani da shi ga lafiyar ka.

Ya na dauke da sinadarin 'dimeric flavonoid' wanda a ke ganin ya na yin magunguna da dama. A yau za mu fada muku manya-manyan amfanin namijin goro.

A na noman wannan dan itace ne a kasashen Najeriya, da Kamaru, da Ghana, da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, da Benin, da Kwadebuwa, da Gabon, da Saliyo, da Laberiya, da kuma Sanegal. Mutanen Afirka sun dade da gano amfanin namijin goro ga lafiya.

A tarihance, likitoci a Afirka sun yi imani cewa, namijin goro na da sinadarin yakar kaska, da yashe ciki, da kuma yakar kananan kwayoyin cuta. Da farko dai likitoci na amfani da shi don maganin tari da cututtukan makogwaro, da bututun iska, da ciwon kai ko sanyin kirji, da kuma ciwon ciki.

Bugu da kari, tsarin maganin gargajiya na Afirka ya nuna masu matsalar hanta ka iya tauna namijin goro.

Wannan dan itace na taimaka wa wajen maganin dukkan nau'i na tari, a na kuma amfani da shi wajen maganin sanyi.Yawanci kuma ya fi amfani wajen kakkabe mashako, da tari, da toshewar hanci, da kuma majina.

Namijin goro ya na taimakawa wajen yakar miyagun cututtuka  ya na kuam dauke da sinadaran yakar dadewar fata da sauransu. Ya na kara karfin kwaranyar jini ga mutanen da ke da matsala da bututun da ke dauko jini daga zuciya.

Sannan ya na taimaka wa garkuwar jiki,domin binciken kimayya na musamman ya tabbatar da cewa, yawan amfani da shi na ba da kariya ga garkuwar jikin dan adam.

Har ila yau Namijin goro na warkar da ciwon gwiwa wajen rage mata radadi sosai yana kuma amfani wajen jin yunwa sannan ya na sa jin kishirwa.

Kammalawa

Mutanen Afirka sun dade da gano amfanin Namijin goro. Su na amfani da shi don dalilai da yawa. Tsarin magungunan gargajiya na Afirka na amfani da namijin goro don maganin cututtuka masu yawa. Duk da haka ya kamata mutane su tuntubi likita kafin amfani da namijin goro don kare lafiya.

Daga taskar
Dr Kabeer ishaq
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com

Monday, 26 March 2018

MATSALAR SANYI (Infection) DA MAGANINSA


Idan mace tana fama da kaikayi ko kuraje ko fitar farin ruwa mai wari ko bushewa ko daukewa ko budewa da kwailewa da rashin sha'awa ko gamsuwa da sauran cututtukan sanyi, sai a gwada daya daga cikin wadannan hanyoyi.
1)A samu Saiwar Garafuni da Sassaken Magarya, sai a tafasa, idan ya dan huce sai mace ta dinga kama ruwa da shi. Kullum sau daya.
Yana maganin budewa da kaikayi.
2) A samu Garafuni da Sassaken Sanya sai a tafasa,
Sai mace ta dinga shan rabin kofi da safe, rabi da yamma.
Yana fitar da dattin mara da maganin farin ruwa mai wari.
3) A samu Furen Tumfafiya, sai a shanya ya bushe, a daka a dinga zubawa a cikin Nono ana sha.
Yana magance matsalar ruwan infection.
.
4) A samu Lalle da Ganyen Magarya da Kanumfari, a hada waje daya a daka sannan a tafasa a zuba farin miski a ciki. Idan ya dan huce sai ta shiga ciki ta zauna tsawon kamar minti goma.
Yin haka yana maganin kaikayi da kuraje da budewa da dadewar gaba.
5) A samu Kabewa a dafa ta, bayan an dafa sai a tsame daga ruwa a jajjagata ko a birga, a zuba Madara ko Nono sannan a sa Zuma a sha.
Wannan yana mganin rashin sha'awa da bushewa da rashin gamsuwa.
6) A dafa Zogale, idan ya dahu sai a murje shi ko a dama, a tace, a yi lemon juice da shi.
Yana maganin fitar farin ruwa mai wari da cushewar mara kuma yana kara ni'ima.
7) A samu `Dan-Tamburawa da Albabunaj a tafasa a zuba Man Hulba a ciki.
Sai ta dan tsuguna tururin ya dinga shigarta.
Idan ya dan huce kuma sai ta shiga ciki ta zauna.
Zai magance mata kaikayi da kuraje kuma yana sa matsewa.
8)A samu Farar Albasa da Kanumfari da Citta da Malmo da Barkono da Raihatul Hubbi,
sai ta dake su tayi Yaji ta dinga cin abinci da shi.
Yana saukar da ni'ima da magance duk
matasalolin sanyi.
9)A samu Sabulun Zaitun da Sabulun Habba sai a daka su.
A samu ganyen Magarya da Garin Bagaruwa a daka a tankade.
Sai a zuba akan sabulan da aka daka sannan a kwa6a da Ma'ul Khal, a zuba Man Tafarnuwa da Farin Almiski.
Sai mace ta dinga kama ruwa da shi kullum sau daya.
Da ruwan dumi amma ake tsarki da shi. Wannan Sabulu yana maganin kuraje da kaikayi da fitar wari.
10) A samu Man Zaitun da Man Habba da Man Tafarnuwa da Man Kanumfari sai a hadesu waje daya.
Mace ta dinga shan cokali daya kullum kafin ta karya.
Yana wanke dattin mara kuma yana samar da ni'ima.
11) A samu Ciyawar Kashe-Zaqi da Farin Magani sai ta hada waje daya ta dinga jika rabin karamin cokali tana sha. Sannan ta dinga shan Man Zaitun Cokali daya kullum kafin ta karya.
Wannan yana maganin dattin mara da wanke daudar mahaifa.
-----------
ABUBUWAN DA SUKE KAWOWA MATA CIWON SANYI KO INFECTION.
1)Rashin sanya pant.
2)Barin pant yayi dauda sosai ba a canja ba.
Ana so in da hali kullum a canja pant sau biyu a wanke.
3)Saka pant a jiqe da ruwa.
4)Yawan tsarki da ruwan sanyi.
5)Yawan tsarki da ruwan da zafinsa yayi yawa.
6)Rashin aski.
7)Wasa da gaba.
8)Yawan cin `Danyar Albasa.
9)Yin amfani da Magungunan mata marasa inganci.
10)Dadewa akan Masai ko toilet.
11)Rashin shan iska.
12)Musanyar tufafi.
13)Saduwa da mai cutar.
12)Cutar Aljanu, wato Jinnul Ashiq. Su ma suna sanyawa mace infection mai wuyar magani.
-------------
ILLOLIN DA SANYI KO INFECTION YAKE YI WA MATA
1)Yana sa Rashin Sha'awa.
2)Yana sa ciwon mara mai tsanani.
3)Yana haifar da kurajen bakin mahaifa ko ya toshe mahaifar baki daya.
4)Yana sa mace ta dinga jinin al'ada baki kirin mai wari.
5) Yana sanya farin ruwa mai wari ya dinga fito mata.
6)Yana sanyawa a dinga jin mace tana wari mara dadi kuma a rasa ta ina yake fitowa duk wankanta.
7)Yana sa jin zafi yayin saduwar aure ko kuma ganin jini a maimakon ruwa.
8)Yana rikitawa mace kwanakin al'adarta, su dinga karuwa ko raguwa ko jinin ya dinga wasa.
9)Yana sanyawa mace tusar gaba, wato iska ta dinga fita ta gabanta.
10)Yana sanyawa mace yawan `Barin ciki ko kuma rashin shigar cikin kwata-kwata.
11)In yayi karfi yana hana mace haihuwa.
12) Wani infection din alama ce ta zaman Aljanu a jikin mace, musamman idan tana mafarkin namiji dare ko jarirai.
Abin lura:-
Idan mace tayi magungunan Asibiti
da kuma irin wadannan da mu ka ambata amma infection din bai warke ba,
To ta nemi maganin jinnul Ashiq, wato magungunan Aljanu don zai iya yiwuwa matsalarsu ce.
Allah yasa a dace.    

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
08096343188' "08165341087"

Friday, 19 May 2017

ZUWAGA MA'AURATA

ZUWAGA MA'AURATA
*****************************
Ayau za mu dan tabo wasu daga cikin
amfanin turaren Almiski, Tafarnuwa,
Alkama, Ayaba da sauransu, wanda mafi
yawan mutane ba su sani ba. Masana sun bayyana amfanin wadannan sirran
da kayan marmari ta bangarori da dama,
musamman wajen inganta sha’awa a
yayin ibadar aure.
An hakkake cewa turaren Almiski yana
taka muhimmiyar rawa wajen motsawa ma’aurata sha’awarsu a yayin da suka
kuduri aniyar gabatar da juna wajen
ibadar aure. Hakan ta kasance ne dalilin
irin kamshin da turaren yake da shi, saide
turaren miski sunanan kala dayawa
amma maikyan shine wanda ake ƙira ( Almisk attahara) yanada ƙauri sannan
farine kamar madara wannan yanada
ƙamshi sosai kuma yana jimawa ajiki
tareda jan hankalin maigida zuwa kanki,
sannan mata suna amfani dashi bayan
sun gama haila domin yaɗauke duk wani ƙarni atareda su.
- Tafarnuwa: Ita ma tafarnuwa shakka
babu
babbar jagora ce wajen samun karfin
jima’i
da kuma dadewa. Galibi ma’aurata sukan fuskanci matsalar sadar da juna a yayin
ibadar aure. Matukar an fuskanci hakan,
za a iya amfani da wannan sinadarin
wajen kara
ni’ima da jimawa a yayin gudanar da
ibadar kamar yadda mukayi bayani a rubutun baya.
- Albasa: A yayin wasu sinadaran ke
amfani
wajen dadewa a yayin jima’i, masana
sun
tabbatar cewa albasa tana daya daga cikin
nau’o’in sinadaran da ake amfani da su
wajen karin yawan ruwan maniyyi a jikin
dan adam. Haka kuma masanan sun
tabbatar cewa Albasa tana taka
muhimmiyar rawa wajen karin girman al’aura musamman ga maza.
- Alkama: Garin alkama na daga cikin
nau’o’in abincin da ma’aurata ke bukata
wajen karin ni’imar aure. Yadda ake
sarrafa shi kuwa shi ne, ana samun garin
alkama a hada shi da nono mai kyau, ko madarar shanu, wadda aka tatsa yanzu-
yanzu, a rika hadawa da ruwan dumi ana
sha. Hakan yana magani sosai wajen
mu’amala tsakanin mata da miji,
musamman kara dadewa a yayin jima’i.
- Ayaba: An kwadaitar da ma’aurata su yawaita cin ayaba, masana sun tabbatar
cewa ita ma Ayaba tana karawa namiji
karfi matukar gaske.
Jirjir: Yana matukar amfanin musamman
ga maza, idan aka hada shi da
Habbarashid, yana kara karfi sosai musamman ma ga wanda yake da rauni
sosai.
- Dabino: Masana sun kwadaitar da
ma’aurata, musamman maza su yawaita
cin dabino gabanin fara ibadar aure. Sun
tabbatar cewa matukar mutum ya ci dabino kwara goma, kafin fara jima’i
gaskiya baza aji kunyaba.
- Habburrashad: Masana da dama sun
kwadaitar da mata su yi amfani da
wannan sinadarin wajen samun karin
ni’ima a jiki. - Hulba: Wannan sinadarin yana da kyau
ga
mata su yi amfani da ita. Su rika sha zai
kara
wa mata ni’ima a jiki sosai.
- Ridi: Maza masu fama da raunin mazakuta suna iya amfani da Ridi, su
yawaita cinsa, yana amfani sosai wajen
magance raunin na su.

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
08096343188, 08165351087
Email- mkabeer5618@gmail.com

Wednesday, 17 May 2017

magungunan Islamic chemist


Ana dafa albabunaj tare da zuma a sha, aljani zai bar jiki nan take in shaa Allah, musamman ga wadanda  suke cikin kai da bargo da jijiya, amma ana son yawan shan ruwa idan ana shan maganin.
08096343188

AKIRU-KARHA

Za a hada shi da zuma a bawa mai farfadiya da safe kafin yaci komai da kuma da marece akalla kwana talatin, bayan sati daya sai a bashi filisko. Zai warke da yardar Allah.
08096343188:

KASHU(yazawa)

Ana shan sa don magance cutar da aljani ko sammu ko maita suka sa a cikin hanta ko zuciya da yawan wasuwasi da kasala da tari da asma , kada a yawaita cinsa.
[08096343188

ZA'AFARAN

Yana halaka bakin aljani tare da halaka mai aljani taurin kai, sannan kuma ya bude idon wanda aljanu suka rufewa ido, ana hada shi da hububul miski da ma'u wardi ana amfani da shi kowane lokaci.
08096343188

HABBAT SAUDA

Aljannu basa sonta ko kadan, wanda yake aiki da ita ma zai samu kariya daga kowane irin mugu, ana kuma hada ta da man zaitun a sha a shafa, sannan ana turara garin ta a cikin agida ko kanti safe da yamma,
haka kuma za'a iya hadawa tare da zuma don magance cutar jiki da dai makamantan su. Zaki iya turara farjinki da ita zaki sha mamaki.
08096343188

MISKI

Idan aka hada man zaitun da miski da habbat sauda aka yi addu'a a ciki ana shafawa yana karya lagon duk wani mugu har mahassadi da maye da boka duka in shaa Allah.
08096343188

DABINO

Yana magance rashin jinin da aljanu suka tsotsa,musamman dabinon madina, amma duk wanda aka ci yayi, sannan yana dawo da ganin da yayi rauni da yardar Allah....] ‪08096343188

YANSUN

Ana dafa shi da zuma da akiru karha a sha don kona bakin aljani mai taurin kai ko fitar dashi daga jiki, sannan yana warkar da sammu da maita da farfadiya da yardar Allah] ‪08096343188

KUSTUL HINDI

kala biyu ne :
Akwai fari da baki
Kowanne aka samu za'a yi aiki da shi wajen warkar da kumburin mahaifa, cizon maciji ko cizon kunama, da duk wata cuta da aljanu ke sakawa dan adam, ko
sammu ko maita, ana shansa da zuma ko a hada da man zaitun, sannan za'a iya daka shi sai dinga shaqa garin ta hanci.

Saturday, 8 April 2017

HERBAL DIET SUPPLEMENTS

HERBAL DIET SUPPLEMENTS

Herbal supplements are a type of dietary supplement that contain herbs. An herb (also known as a botanical) is a plant or plant part used for its scent, flavor, and therapeutic properties.
Diet supplements derived from herbs usually contain more than one type of herb. The purpose of an herbal diet supplement is to increase the benefits that you get from your normal diet and to ward off the negative effects. Herbal diet supplements are rich in vitamins, minerals, amino acids, etc. Obviously, dietary supplements are not meant to be used as treatments or cures of any disease or medical condition. They are more effective as preventative agents that help strengthen the body and the immune system to naturally ward off any infections or internal malfunctions. For people who do not manage a balanced diet herbal diet supplements also supply necessary nutrients missing from regular diet.

Many herbal dietary supplements can provide substantial aid for different types of medical conditions.
Some herbal diet supplements are:
·     Ephedra. This supplement increases the body resistance towards common cold, helps in the treatment of asthma and upper respiratory problems. For people who work out regularly, ephedra is an important ingredient in most fat loss supplements.
·     Magnesium. Minerals and salts are the biggest deficiencies in an unbalanced diet. Magnesium is essential in preventing kidney, thyroid, and heart disease. There are many herbal diet supplements rich in magnesium.

·     St. John's wort. Also known as hypericum, Klamath weed, and goat weed, this supplement has been used for centuries in the treatment of mental disorders, nerve pain. In older times it was also used as a sedative and malaria cure. Nowadays, the common uses are treatment of depression, anxiety, and sleep disorders. It is typically consumed as a tea or in pill form.
                
·     Vitamin E. Uncontrolled oxidation in our body can result in long-term damage. That is why our bodies generate anti-oxidants. However, if the production of anti-oxidants falls below safe levels then external supplements are required.
·     One very potent anti-oxidant is vitamin E. Herbal diet supplements rich in vitamin E make good anti-oxidants.
·     Copper. While metals and minerals are essential to the normal functioning of our body, sometimes they can fail to get absorbed properly. Zinc is essential for our body and there is nothing better than a copper rich herbal diet supplement. These supplements increase the absorption of zinc. The result is better protection against heart disease, and healthier skin and hair color.

·     Folate. From a certain viewpoint, folates are required more than anything else because they can affect us down to our DNA. Folates are required for the production and maintenance of new cells (especially during pregnancy and infancy). DNA replication cannot take place without folates. Folates also prevent cancer causing DNA changes. Folate deficiency affects the bone marrow where most new cells are produced. Folates are needed to make new red blood cells and prevent anemia. As you can see, any deficiency in folates can be devastating in the end. One of the earliest indications of folate deficiency is anemia. Herbal diet supplements that have folates as major ingredients are always good for you, even if you do not have any problem currently.

·     Iron. In the human body, the metal iron is more pervasive than any other. It plays an important part in several vital functions. Iron carries oxygen to the lungs and muscles in the form of hemoglobin. It acts as a means of transport for electrons between cells. It is a catalyst for enzyme reactions in tissues. Iron deficiency most commonly occurs in children and pre-menopausal women. It can easily prove to be fatal if left unchecked. Herbal diet supplements rich in iron can help to prevent such a situation.

·     Vitamin B6 and B12. Vitamin B6 (pyridoxine) deficiency can lead to anemia, depression, dermatitis, and high blood pressure. Vitamin B12 (cyanocobalamin) deficiency can lead to anemia, memory loss, and cognitive decline. It is most likely to occur among elderly people. In extreme cases it can even cause paralysis can result. It is widely used in the treatment of alcoholism, depression, diabetes, hair loss, and stress. Vegans are especially at risk of B12 deficiency because vitamin B12 naturally occurs only in meats. So if you are a vegan than an herbal dietary supplement with vitamins B6 and B12 is an absolute must for you.

·     Tea. Most herbal teas (and especially Medicinal Strength Teas) involve the use of herbs that have anti-oxidant properties useful in prevention of cancer, heart disease, high blood pressure. Since these teas usually do not involve caffeine and other associated chemicals they are better from a health perspective than regular tea or coffee.

·     Vitamin D. The human body (especially skin) develops its own vitamin D. It is necessary to maintain normal levels of calcium and phosphorous. A direct result of vitamin D deficiency is a weaker skeleton, a condition known as osteoporosis where the bones become porous and hence break easily. Vitamin D herbal supplements can help prevent osteoporosis.

·     Selenium. This is a chemical so volatile that it does not occur in its free state in nature. Toxic in large amounts, trace amounts of it form the center of some enzymes that are vital to the normal working of all cells in nearly all living organisms. In the human body it behaves as an anti-oxidant and is also important for the normal working of the thyroid gland. Cereals, meat, fish, and eggs are good sources of selenium. Since the majority of sources are animal based, vegans and vegetarians should seriously herbal dietary supplements containing selenium.

·     Vitamin A. This vitamin is responsible for maintaining good eye sight and promoting bone growth. It is also an anti-oxidant. Most skin and eye problems are related to vitamin A deficiency so if you have any such conditions, consider a herbal diet supplement rich in vitamin A

daga taskar
Dr kabeer
08096343188