Powered By Blogger

Saturday, 10 December 2016

YADDA AKE RUQYA A MUSULUNCI.

dafarko dai kusani ruqya a musulunci halal ne manzon allah (s.a.w) yayi ruqya, ankarbo daga dan abbas (R.A) cewa wata taje wajen manzon allah tare da danta marar lafiya mai cutar hauka tace ya ma,aikin allah wannan yaronane yana damunmu da ta,adi da barna sai annabi ya dafa kirjin yaron yayimasa ruqya kuma yabuda bakinsa yayimasa toti aciki sai akaga wani abu baki wulik yafito daga bakin yaron take yatashi yasamu sauki ahmad da darumi ne suka rawaito hadisin KA,IDODIN RUQYA Wajen da za,ayi ruqya yakasance mai tsarki wurin yakasance babu kowa daga marar lafiya sai danginsa, idan macece dolene ta saka hijabi da dogon wando dan kar aljani yabaiyana ya bude mata tsiraici kayiwa marar lafiya da danginsa bayanin kai mai addu,a ne kawai, amma waraka tana wajen allah, afitar da duk wani photo dayake cikin dakin, ko yar tsana ko gunki ko wani zani mai almar foton mutum, domin duk wayannan abubuwa suna hana shigowar mala,iku (hadith) akarbe duk wani abu dayake jikin marar lafiya wanda yasabawa shari,a. GA ABINDA AKAFISO AKARANTA A RUQYA DAGA AYOYIN AL-QUR,ANI Amma wajibine kasani cewa dukkan ayoyin al-qur,ani warakane ga mutane ta,awizi da basmala fatiha aya 5 ta farkon suratul bakara ayoyi 2 tsakiyar suratul bakar, daga (wa ilahukum ilahuwahid), amanar rasulu akarshen suratul bakara, shahidallahu acikin suratul alimran daga aya ta 18-19 inna rabbakumullah, acikin suratul a,araf aya ta 54-56 afa hasibtum, suratul muminin aya ta 115-118 wa annahu ta,ala, suratul jinni aya ta 3-9 aya 10 na farkon suratul saffat, aya uku na karshen suratul hashri, aya ta 21-23 kulhuwallahu da falaki da nasi 3-3.,, domin annabi (s.a.w) yayi amfani da wadannan ayoyi ga marar lafiya kuma yasamu waraka amma inkaso zaka,iya amfani da qur,ani dukkansa waraka ne.... Muhdu a darasi nagaba

Daga taskar
Dr kabeer gidanmagani
08096343188, 08165341087
mkabeer5618@gmail.com
Www.gidanmagani.wordpress.com
Www.gidanmagani.blogspot.com

DALILAN DA YASA JINNU SUKE SHAFAR MUTUM

akasarin jinnu suna shafjr mutum ne saboda daya daga cikin wadannan dalilai dasunan kauna ko ma aure ga mace ko namiji saboda zalunci da mugunta saboda zaluncin da dan adam yayimusu kamar zuba ruwan zafi ko yatakasu idan bokaye da matsafa sun turosu.. LOKATAN DA JINNU KE SHIGA JIKIN DAN ADAM. lokacinda mutum yatsorata, lokacinda mutum yake cikin matsanancin bacin rai da fushi, lokacinda mutum ya nutse cikin sabon allah kamar kallace kallacen finafinan batsa, lokacin da mutum ya nutse cikin tsananin nishadi da masha,a, lokacinda mutum yake cikin janaba ko haila ta mata... ALAMOMIN SAMUWAR ALJANU AJIKIN DAN ADAM Yawan mantuwa mai tsanani, samun damuwa da kuncin rai mutuwar wani bangare najikin mutum cizon hakori a barci, jin wani motsi kamar anabinka abaya yawan kokwanto firgita abarci, yawan mafarkin saduwa babisa ka,idaba yawan zubar jinin haila ba ka,ida jin sauti kamar ana kiranka, da makamantansu

Saga taskar
Dr kabeer gidanmagani
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com
Www.gidanmagani.wordpress.com
Www.gidanmagani.blogspot.com

MATSALAR ALJANNU DA RUQYA

HALITTAR JINNU. Jinnu halitune da allah ta,ala yayi domin subauta masa yakuma ajiyesu a duniya, kuma allah ya haliccesu daga harshen wuta allah yace "kuma yahalitta aljani daga (BIRA) ta wuta (harshen wuta) dan abbas yace lallai aljanu anhaliccesu daga harshen wuta. Dan haka sai muce jinnu wasu halittune da allah yahaliccesu daga harshen wuta shiyasa ba,a ganinsu kuma ba,a iya tabasu ko jin motsinsu, saboda su ruhine kawai basuda tabbataccen gangar jiki irinna dan adam shiyama suke iya rikida izuwa duk surar da sukaga dama, kamar kare, maciji, kyanwa, da sauran halittu.. Allah ta,ala ya halicci jinnu nau,in halittu mabambanta. Hakim yarawaito hadisi daga aba sa,alatal kushaniyya yace manzon allah (s.a.w) yace aljanu nau,i ukune, akwai masu fuka fukai suna tashi sama, da masu zama macizai da kunamai, da kuma masuzama waje daya su kaura.

Daga taskar
Dr kabeer Gidanmagani
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com
Www.gidanmagani.wordpress.com
Www.gidanmagani.blogpost.com

Friday, 9 December 2016

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA KASH NA2I

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA (iyayen giji ) 2

Idan mace tana bukatar maniyinta yakaru, sai tasami madarar shanu kofi 1 tazuba man tafarnuwa karamin cokali 3 tasha sau 2 arana zata samu karin ni,ima nantake tabaiwa megida mamaki. MATAR DA TAKESO GABANTA YA MATSE; tasami wani turare maisuna (misk al-gazali) daya bisa hudu na karamin cokali ahada da man tafarnuwa karamin cokali atsoma auduga tasa agabanta tayi kunzugu ayihaka kwana 4 ko 5, zatakoma kamar budurwa...@{ amma aji tsoron allah}..

Daga taskar
Dr KABEER ISHAQ

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MATA (iyayen giji)

Gaeme da matarda bata taba haihuwaba idan tanaso tagane zata iyasamun ciki? Ko a,a? To sai tasamuwa mai dumi da sabulu tawanke gabanta sosai sannan tasamu auduga maikyau sannan tazuba man tafarnuwa cokali daya akan audugar sannan tayi kunzugu da audugar har tsawon awa 2, intaji warin tafar nuwar abakinta, zatasamu ciki lokacine baiyiba kokuma matsalar daga mijinne inkuma batajiba to sai dai allah yasawake, amma ana maimaitawa har sau uku domin kara tabbatarwa.. YAWAN LALACEWAR CIKI KO YAWAN BARI; asamu kwan agwagwa asoya da man tafarnuwa abaiwa matar taci sau 2 arana kwana 7. TSAWON GASHI DA HANASHI KAKKARYEWA; Asamu man kwakwa ahada da man zaitun da man tafarnuwa arinka shafawa akai, amma man tafarnuwa 50% za,asa sauran kuma 100&... Allah yasa mudace...

DAGA TASKAR
Dr kabeer ishaq
08096343188, 08165351087
mkabeer5618@gmail.com

AMGANIN MAN TAFARNUWA GA MAZA

AMFANIN MAN TAFARNUWA GA MAZA

idan namiji yanajin kaikayi a marainansa ko a azzakarinsa to sai yasamu garin farar kanwa cokali 1 adafa da ruwa kofi 2 idan ya tafasa sai azuba man tafarnuwa cokali 2 inyahuce sai yawanke gabansa da ruwan zaisamu sauki insha allah

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
08096343188,08165351087
mkabeer5618@gmail.com

ABUBUWAN DA SUKE HANA DAUKAN CIKI


assalamu alaiku wa rahmatullah
In ANAS0 agane dalilin dayakan hana samun ciki ana ganowa ta hanyoyi da dama zamu fadi kadan dagaciki.
(1) idan al aurar namiji yacika kankanta wani lokacin yanahana samun ciki.
(2) idan yanayin al,aurar namiji yacanza ta yadda maniyi bayafutowa sai dakyar yanahana samun ciki.
(3)damuwa mai tsanani ko rashin kxanciyar hankali ga mace yana hanata samun ciki
(4)idan mace tana yawan yin kaho yana hanata daukan ciki.
(5) idan akarasa dalilin rashin samun ciki sai ashuka dawa ko GER0 sai a umarci mace tarika yin fitsari akan wannan shuka idan shukar tafito to zata iya samun haihuwa inkuma batafitoba to sai addu,a. (wallahu a,alam)
(6) asamu kofi azuba ruwa acikinsa sannan azuba maniyin namiji acikin ruwan idan maniyin yataso saman ruwan to maniyin ba mai haihuwa bane sai anemi magani. wallahu a,alam
xantsaya anan muhadu a kashi na 2
<[=DR KABEER=]>