MUHIMMAN MAGUNGUNA ASAUKAKE
Daga taskar
Dr kabeer ishaq
08096343188
GWANDAR DAJI
Sassaken gwandar daji yana
1-maganin tsutsar ciki,
2-zawo, ciwon ciki,
3-saran maciji,
4-ciwon baki da ciwon hakora.
Sassaken, hadi da sansami (kunnuwa) suna:
1-maganin hakarkari,
2-fuka,
3-Asma,
4-ciwon gabbai.
Saiwar gwandar daji (Saye) tana maganin
1-sanyin mata,
2-gurkutar ciki.
Sauran bangarorin bishiyar suna maganin
1-ciwon idanu da fata.
TUMFAFIYA
Tumfafiya tana
1-wanke ciki,
2-Tana maganin makero, kyasfi, kurkunu, kurajen zufa,
3-Asma,
4-cizon kunama, tunjere da ciwon idanu.
Saiwar tumfafiya tana
1-maganin cizon maciji.
NAMIJIN YADIYA
Namijin yadiya ruwansa na maganin
1-zanzana, irinsa kuma, na
2-maganin ciwon idanu.
ADUWA
Sassaken aduwa da ‘ya’yanta suna
1-maganin fitsarin jini, kurkunu,
2-ciwon farfadiya,
3-Rashin haihuwa da ciwon hauka.
SANSAMI (Jiri)
Sassaken sansami, saiwa, da gidan irin suna maganin
1-gyambo, kuraje,
2-kuturta,
3-sanyin mata
4-Tari.
ISKICI
Sassaken iskici yana maganin
1-cizon kunama, cizon maciji,
2-masassara da
3-ciwon ido.
Saiwar Iskici kuma na maganin
1-ciwon ciki da
2-Tsutsar ciki.
ANZA
Sansamin anza, yana maganin
1-Ciwon Ido,
2-Fitsarin jini,
3-Ciwon ciki,
4-kuraje, kurkunu, da
5-Fitar baya (Basur).
‘Yayanta kuma na maganin
1-Ciwon tunjere.
NAMIJIN TSADA
Saiwar namjin tsada tana maganin
1-cizon maciji,
2-ciwon tunjere,
3-ciwon ciki, kuturta,
4-Diddira
5-karfin maza.
Sansaminsa suna maganin
1-ciwon hakora,
2-Tsutar ciki,
3-ciwon ido,
4-Rashin samun haihuwa ga mace,
5-kuraje da wankin ciki.
SABARA
Saiwar sabara tana maganin
1-zawo da diddira
Sassaken sabara yana maganin
1-ciwon ciki.
Sabara Da Sansaminsa suna maganin
1-Tari, mashasshara da ciwon ciki.
KAIWA
Sassaken kaiwa yana maganin
1-kuraje da Gyambo.
Saiwarta tana maganin
1-Diddira,
2-Tsutsar ciki,
3-Mashasshara,
4-Hakarkari,
5-Tunjere da kuraje.
MALGA
Saiwar malga tana maganin
1-sanyin mata,
2-Diddira,
3-Fitar baya,
Malga Da Sansami suna maganin
1-Masassara,
2-Gyambo da kurajen baki da na dasashi.
KIRYA
Kirya tana maganin
1-ciwon kai,
2-ciwon haure,
3-ciwon amosanin kashi,
4-ciwon fata,
5-masassara da diddira.
DOGON YARO (Darbejiya)
Sassaken dogon yaro kunnuwa da mai suna maganin
1-masassara,
2-ciwon fata,
3-sanyin mata,
4-ciwon amosanin kashi, da
5-ciwon tsutsar ciki.
MADACI
Sassaken madaci yana maganin
1-shawara,
2-cizon kunama
3-ciwon tsutsar ciki.
Madaci da iri da sansami, suna maganin
1-masassara da ciwon kai.
Saiwa tana maganin
1-Rashin haihuwa, da
2-ciwon hauka, da
3-karfin maza.
ZOGALE
Zogala tana maganin
1-ciwon amosanin kashi,
2-kurajen zufa,
3-ciyon dasashi,
4-shawara ciwon kai,
5-sanyin mata, da
6-Tunjere.
MAGARYA
Magarya tana maganin
1-Tsamukar ciki,
2-ciwon gaba,
3-ciwon hanta.
Daga taskar
Dr kabeer ishaq
08096343188
No comments:
Post a Comment