Amfanin Iccen DARBEJIYA
**************************
Darbejiya Ana kiran iccen Darbejiya da dogon yaro da turanci kuma ana kiransa da neem tree a India kuma suna kiransa da Margosa a wani wajen kuma Lilac.
Darbejiya nada Amfani sosai, a Africa ta tsakiya suna kiransa da muarubiani wato maganin cuta arba'in.
A india anfi shekara 500 ana amfani da ganye, 'ya'ya da itacen darbejiya a matsayin magani....
Iccen Darbejiya gaba dayansa maganine kama daga ganyen sa 'ya'ya da Sassaken sa, sannan ana samun mansa ne daga 'ya'yan sa.
Iccen Darbejiya yana maganin citutukka da yawa kamar su; Masassara, Malaria, gyambo, da matsaalolin fata.
Man Darbejiya, na taimakawa jikin dan Adam wajen yaki da Fungals, Bacterias, da sauran cutukka masu takurawa dan adam, kuma yana magani ciwon gabobi.
YADDA ZA'AYI AMFANI DA DARBEJIYA;
----------------------------------------------------
MAKERO, HAWAN JINI
~~~~~~~~~~~~~~
A samu ganyen darbejiya ayi Juice dinsa a riqa shan kofi daya duk safiya DOMIN magance matsalar hawanjini.
A riqa shan rabin kofi na juice din darbejiya duk safiya domin magance makero.
GYARAN JINI
~~~~~~~~
Shan Juice din ganyen darbejiya na tsaftace jinin Dan adam, za'a iya cin ganyen darbejiya guda goma duk safiya har kwana goma sha biyar wannan yana magani da yawa a cikin jikin dan adam.
LAFIYAR HAKORI
~~~~~~~~~~~
A shanya kunnuwan darbejiya a inuwa idan sun bushe a hada da gishiri da kuma kanunfari a riqa brush da wannan hadin yana maganin KURAJEN BAKI, WARIN BAKI, sannan yana saka hakora haske da karfi.
KURAJEN ZAFI
~~~~~~~~~
A tafasa kunnuwan darbejiya a ci sannan marar lafiyar ya kwanta a saman ganyen na darbejiya, ariqa yi ana cenja ganyen a kwana 3 za'a samu lafiya In shaa Allahu.
KURAJEN FUSKA
~~~~~~~~~~
A daka ganyen darbejiya duk dare a shafa in za'a kwanta bacci idan aka tashi da safe a wanke da ruwan sanyi.
KYASFI KO MATSALOLIN FATA
~~~~~~~ ~~~~~~~~~~
A daka ganyen darbejiya a hada da zuma a shafa.
KARYEWAR GASHIN KAI.
~~~~~~~~~~~~~~~
Asamu ganyen Darbejiya da ganyen lubiya a tafasasu a ruwa a wanke kai da ruwan idan an gama a shafa man darbejiya, Wannan yana maganin kakkaryewar gashi, yana saka gashi baki, kuma yana saka shi tsawo sannan yana maganin matsalolin gashin kai.
AMAI
~~~~
Domin tsayar da Amai a samu ganyen darbejiya a saka shi a cikin ruwa awa daya a debe a sha kofi daya yana saurin tsayarda amai.
Gudawa
~~~~~~
A zuba man darbejiya a cikin shinkafa a ci yana saukar da gudawa.
ZUBEWAR GASHIN GIRA
~~~~~~~~~~~~~~~
A murza ganyen darbejiya a gira yana maganin zubar gashin gira.
CIWON KUNNE
~~~~~~~~~
A tafasa ganyen darbejiya idan ya tafasa a sauke idan ya huce a riqa digawa a kunnen da ke ciwo.
BUSHEWAR LEBO
~~~~~~~~~~~
A hada Man darbejiya da man ridi a riqa shafawa a labba (lips).
CIWON MARA LOKACIN AL'ADA
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
A jiqa citta idan ta jiqu a hada da juice din darbejiya a sha kofi daya yana kawar da ciwon mara lokacin al'ada.
DOMIN DAFI
~~~~~~~~
Idan kare ko maciji ya ciji mutum idan ana so a gane cewa akwai dafin a jikin mutum a bashi ganyen darbejiya ya ci idan yafi dacinsa to ba dafin a tare da shi, idan kuma bai ji dacin sa ba to akwai dafin a jikin sannan kuma a samu ganyen darbejiya dana lubiya yana ci wannan yana kawar da dafi kowane irine a jikin mutum.
ABIN LURA;
************
Kada wajen amfani da shi a bari ya shiga ido.
In shaa Allahu zuwa gaba zan kawo muku yanda ake hada shi domin masu fama da cutar Qanjamau, Cancer, da sauransu.
Godiya Ga Allah da yayi cuta yayi Magani.
Ya Allah ka kara mana Lafiya wayanda basu da lafiya kuma ka basu,,,,(Ameen)