Powered By Blogger

Wednesday, 5 June 2019

MATSALAR OLSA

OLSA

Wannan ciwo ya kasu biyu:
1-Olsa mai kama qirji shine saman uwar hanji.
Image result for acid reflux ulcer
Alamominta: ciwon qirji, saurin jin yunwa, da xaurewar qirji tokarewar nunfashi, da zafin jiki da zazzavin lokaci-lokaci.
Idan tad axe a jikin mutum zata haddasa buguawar zuciya da xumin ciki da gigicewa da kasala da vacin rai.
Maganinta: Sai a sami dakakken garin alkama da garin almawafiq a ringa sha da Nono ko madara fik sau uku a rana.
2-OLSA MAI KAMA CIKI:
Image result for stomach ulcer
Alamominta: sun haxa da xaurewar ciki da xuminsa jin yunwa akai akai, damuwa da saurin fushi da xaurewar ciki zuwa gindin cibiya.
Maganinta: Sai a sami barkono "Tsiduhu" sai a sami kabeji zogale sai a hada da kayan yaji a daka sai a ringa ci sau uku a rana abinci.
Ko kuma a nemi bagaruwa a dakata a haxa da gujiya sai a daka a ringa sha a madara fik.
Ko kuma a nemo ganyen zogale da habbatus-sauda a ringa shansa a shayi ba madara ko kuma a nemi tuffa a dakata da dabino sai a ringa ci safiya da dare.
Ko kuma a daka xanyar shinkafa da zogale a ringa ci a abinci.
Ko kuma a samo sassaqen faru a daka shi da kayan qamshi za'a warke. A ringa ci a abinci.
Abincin da ake so mai Olsa ya ringa ci shi ne:
'yan ringa cin abinci mai xabi'ar baridi (sanyi) kamar salak kwaxo ko kwaxon zogale ta rama da yawan cin shinkafa 'yar gida. Waxannan suna daga cikin abinci mai xabi'ar sanyi.
Abubuwan da mai Olsa zai guda.
Lallai ne ya daina cin abu mai zafi rau da mai sanyi qarara ya nisanci cin jan nama ko ya rage cinsa ya nisanci cin abin mai maiqo ko nama mai kitse.
Kuma da yaji yunwa ya nemi abinci kada ya bari sai cikinsa ya fara qullewa.
Idan Olsa tai qarfi tana iya haddasa yawan hamma vacin rai tsorata haka kawai, damuwa da ka da kasalar jiki daka ci abinci sai ka ji bacci kake so.

08096343188