Powered By Blogger

Monday, 16 January 2017

NAMIJIN DARE

NAMIJIN DARE
---------''----'----------'''-------------------

Dayawan lokaci ana samun mace ko namiji wanda aljanu suke aura aita fama arasa magani. Allah yakara tsaremu ...

     inhakan yafaru ga mace ga mafita insha Allah

Asamu sassaken iccen kadanya     sannan asamu MUNUMUNU wata kunama ce baka asameta matacciya sai asamu tururuwa wacce akecewa gwano shima matacce ahada da wannan kunamar akonasu sai adebi tokar ahada da kitsen akuya adaka shikuma wannan iccen kadanya jikashi za'ayi amma anfiso ayi amfani dasu alokacin akayi tsarkin haidha  bayan anyi tsarki sai adauko wannan iccen da akajika ayi wanka dashi sannan kafin ruwan yabushe sai ayi turare da wannan turwa kunama da kitse wanda akahada
In akayi haka sau daya aranar farko shikenan sauran ranekun kuma sai ayi tsarki da ruwan maganin sannan shikuma wanda akahada da kitsen ayi turare a tsuguna     za'a  rabu dashi in Allah yayarda
  wannan magani sahihine
Akan irin wannan matsala insha Allah

Wanda ya amfana da wannan magani goronsa yayiwa annabi salati

Daga taskar
Dr kabeer ishaq
Domin karin bayani atuntubemu ta whatsapp
📞08096343188  ko  ☎08165351087
ko email-  mkabeer5618@gmail.com
  Visit our website blog
www.gidanmagani.blogspot.com

Thursday, 12 January 2017

AMFANIN ICCEN DARBEJIYA

Amfanin Iccen DARBEJIYA
**************************
Darbejiya Ana kiran iccen Darbejiya da dogon yaro da turanci kuma ana kiransa da neem tree a India kuma suna kiransa da Margosa a wani wajen kuma Lilac.
Darbejiya nada Amfani sosai, a Africa ta tsakiya suna kiransa da muarubiani wato maganin cuta arba'in.
A india anfi shekara 500 ana amfani da ganye, 'ya'ya da itacen darbejiya a matsayin magani....
Iccen Darbejiya gaba dayansa maganine kama daga ganyen sa 'ya'ya da Sassaken sa, sannan ana samun mansa ne daga 'ya'yan sa.
Iccen Darbejiya yana maganin citutukka da yawa kamar su; Masassara, Malaria, gyambo, da matsaalolin fata.
Man Darbejiya, na taimakawa jikin dan Adam wajen yaki da Fungals, Bacterias, da sauran cutukka masu takurawa dan adam, kuma yana magani ciwon gabobi.
YADDA ZA'AYI AMFANI DA DARBEJIYA;
----------------------------------------------------
MAKERO, HAWAN JINI
~~~~~~~~~~~~~~
A samu ganyen darbejiya ayi Juice dinsa a riqa shan kofi daya duk safiya DOMIN magance matsalar hawanjini.
A riqa shan rabin kofi na juice din darbejiya duk safiya domin magance makero.
GYARAN JINI
~~~~~~~~
Shan Juice din ganyen darbejiya na tsaftace jinin Dan adam, za'a iya cin ganyen darbejiya guda goma duk safiya har kwana goma sha biyar wannan yana magani da yawa a cikin jikin dan adam.
LAFIYAR HAKORI
~~~~~~~~~~~
A shanya kunnuwan darbejiya a inuwa idan sun bushe a hada da gishiri da kuma kanunfari a riqa brush da wannan hadin yana maganin KURAJEN BAKI, WARIN BAKI, sannan yana saka hakora haske da karfi.
KURAJEN ZAFI
~~~~~~~~~
A tafasa kunnuwan darbejiya a ci sannan marar lafiyar ya kwanta a saman ganyen na darbejiya, ariqa yi ana cenja ganyen a kwana 3 za'a samu lafiya In shaa Allahu.
KURAJEN FUSKA
~~~~~~~~~~
A daka ganyen darbejiya duk dare a shafa in za'a kwanta bacci idan aka tashi da safe a wanke da ruwan sanyi.
KYASFI KO MATSALOLIN FATA
~~~~~~~ ~~~~~~~~~~
A daka ganyen darbejiya a hada da zuma a shafa.
KARYEWAR GASHIN KAI.
~~~~~~~~~~~~~~~
Asamu ganyen Darbejiya da ganyen lubiya a tafasasu a ruwa a wanke kai da ruwan idan an gama a shafa man darbejiya, Wannan yana maganin kakkaryewar gashi, yana saka gashi baki, kuma yana saka shi tsawo sannan yana maganin matsalolin gashin kai.
AMAI
~~~~
Domin tsayar da Amai a samu ganyen darbejiya a saka shi a cikin ruwa awa daya a debe a sha kofi daya yana saurin tsayarda amai.
Gudawa
~~~~~~
A zuba man darbejiya a cikin shinkafa a ci yana saukar da gudawa.
ZUBEWAR GASHIN GIRA
~~~~~~~~~~~~~~~
A murza ganyen darbejiya a gira yana maganin zubar gashin gira.
CIWON KUNNE
~~~~~~~~~
A tafasa ganyen darbejiya idan ya tafasa a sauke idan ya huce a riqa digawa a kunnen da ke ciwo.
BUSHEWAR LEBO
~~~~~~~~~~~
A hada Man darbejiya da man ridi a riqa shafawa a labba (lips).
CIWON MARA LOKACIN AL'ADA
~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
A jiqa citta idan ta jiqu a hada da juice din darbejiya a sha kofi daya yana kawar da ciwon mara lokacin al'ada.
DOMIN DAFI
~~~~~~~~
Idan kare ko maciji ya ciji mutum idan ana so a gane cewa akwai dafin a jikin mutum a bashi ganyen darbejiya ya ci idan yafi dacinsa to ba dafin a tare da shi, idan kuma bai ji dacin sa ba to akwai dafin a jikin sannan kuma a samu ganyen darbejiya dana lubiya yana ci wannan yana kawar da dafi kowane irine a jikin mutum.
ABIN LURA;
************
Kada wajen amfani da shi a bari ya shiga ido.
In shaa Allahu zuwa gaba zan kawo muku yanda ake hada shi domin masu fama da cutar Qanjamau, Cancer, da sauransu.
Godiya Ga Allah da yayi cuta yayi Magani.
Ya Allah ka kara mana Lafiya wayanda basu da lafiya kuma ka basu,,,,(Ameen)

Monday, 9 January 2017

MAGANIN CIWON SANYI NA MATA

MAGANIN CIWON SANYI NA MATA
**************************************
Hakika ciwon sanyi na mata yana daga cikin cututtuka masu wuyar magani, kuma mata da yawa suna shan fama dashi.
Ga wata fa'idah nan daga ZAUREN FIQHU ku jarraba, In sha Allahu za'a samu waraka.
Anemi :
1. Garin Tafarnuwa.
2. Saiwar Raihan (Doddoya - Rai dore)
3. Garin Kanumfari da citta.
4. Saiwar Zogale.
Wadannan abubuwan gaba daya ahadasu adakesu waje guda, sannan arika diban cokali guda ana dafawa ana sha kullum safe da yamma.
Sannan adebi wani ahada da barkono ayi yaaji dashi arika cin abinci. In sha Allahu koda sanyi yayi shekara arba'in ajikinki ko fiye da haka, zaki warke.
Hakanan Mazaje masu fama da matsalar Sanyin mazakuta, Idan sukayi wannan hadin zasu samu waraka da izinin Allah (SWT).
Tukwicin da za'a bani shine ayi Salati guda goma bisa Masoyina, Shugabana, abin koyina, Muhammadur Rasulullahi (Sallal Laahu alaihi wa aalihi wa sallam).

MAGANIN SANYI NA MAZA

MAGANIN SANYI NA MAZA

Shi wannan sanyin gaskiya yana da wahalar jin magani. Domin kuwa wadancan abubuwan da ka ambata a baya, mutane da yawa sun jarraba kuma sun samu waraka da yardar Allah.
Amma ga wasu nan ga jarraba:
1. Ka nemi Man Habbatus sauda dan Misra ko Algeria ko Hemani. Ka gaurayashi da man Tafarnuwa Original tare da Man Albabunaj. Sannan ka rika dafa 'danyar chitta (Ginger) da ruwa kofi guda. idan ya dafu sai ka sanya wancan Man chokali guda aciki, sannan ka sanya zuma daidai gwargwado, sannan kasha.
In dai sanyi ne, kowanne iri ne in sha Allahu zaka samu waraka.
Ka samu Furen Albabunaj (chamomile flower) ka rika dafa cokali guda kana sha kullum da safe. In sha Allah Wannan zai wanke maka Qodarka da mafitsararka, Kuma zai magance maka Matsalolin ciwon sanyi.
WALLAHU A'ALAM.

Sunday, 8 January 2017

AMOSANIN KASHI

Sanyin kashi wato (Oesteo Arthritis).Hanyoyin da ake kamuwa dashi, da kuma kariya daga kamuwa dashi
------------------------------------------
Sanyin kashi, ya sha bam bam da amosanin jini wato sikila,sannan kuma yasha bam bam da sanyin da ake kamuwa dashi ta hanyar saduwa.
Sanyin kashi na gout, wanda ke kama ga6o6i yakan zo ne saka makon wani sinadari na acid da jiki ke sarrafawa bayab munci abinci irinsu jan nama,misali naman shanu,ko na akuya, ko na rago. Ko kuma cin alayyahu.saboda jan nama da alayyahu suna dauke ne da sinadarin acid mesuna (Uric Acid) wanda shi wannan acid din se ya taru a ga6o6i ya rinka cinye ba6o6in ahankali. Se mutum ya fara jin alamu na ciwon. Ga6o6i, da kumburi. Sannan shi wannan ciwon ba sanyi na ruwa ko na korama ke kawo shi ba, sanyin kashi yafi kama yatsun kafa.sannan shi sanyin kashi yana kama kowa da kowa.amman be cika kama yara ba. Yana kama manya, matasa da tsofaffi.sannan ga yara bayasa ga6o6insu ciwo da kumburin kashi, idan kga ga6a 6uwan yaro na ciwo kuma ga6o6insa sun kumbura to wannan alamu ne na sikila.
Shi sanyin kashi nau,i biyu ne
Akwai na gado shi ake kira (Ruematoid Arthritis). Wanda shi wannan gasky ba,a warkewa sai dai samun sauki ta hanyar bashi maganin rage zafi da ciwo da kumburin ga6o6in..sannan idan mutum ya kiyaye cin jan nama da alayyahu to ba zai rinka tasar masa ba. Kuma na gadan yafi kama kana nun ga6o6i, wato ga6o6in kafa dana hannu. sannan
Akwai wanda muke samu daga jan nama, ko alayyahu shi kuma ana ce masa (Osteo Arthritis) shi kuma yafi kama manyan ga6o6i irinsu ga6ar hannuwa data kafa da wuya, shi kuma jan nama ne da alayyahu ke kawoshi
kowa ne sanyin kashi kalar maganinsa daban.dole se kaje asbt a tantanse wanne gareka..
Hanyoyin magance shi
-------------------------------
Dole ne a kiyaye cin jan nama, aci farin nama memako misali naman kaza.zabo,taletale.agwagwa,kifi da sauransu
Sannan a kiyaye cin alayyahu wanda ba me tsafta ba. A wanke shi da gishiri.sannan a sahi a abinci ruwa na tafasa ba se abinci ya dafu ba
Sannan a ziyarci likita ba shan magani barkatai ba

Monday, 2 January 2017

Amfanin Abarba (pineapple)

Amfanin Abarba (pineapple) a jikin dan adam. Musamman ma kare jiki daga kamuwa da ciwon zuciya.
Abarba na daya daga cikin yayan itatuwa masu amfani a jikin dan adam.
Abarba na da matukar amfani a jikin dan adam saboda tana dauke da muhimman abubuwa; fibres,menirals.vitamins.Nutrient da kuma Anti.Oxidant. Wadanda ke da matukar amfani ga rayuwar dan adam.sannan takan kare jiki daga cututtuka.Ga kadan daga amfanin Abarba;
1.tana dauke da sinadarin
magnees da calcium wanda ke kara karfin kashi
2.tana dauke da anti.oxidant wanda ke kara ma jiki lafiya da kare jiki daga saurin tsufa.
3.tana maganin mura da sanyin kirji.
5.tana kara ma garkuwar jiki lafiya da kare shi daga cututtuka
6.tana maganin kamuwa da ciwon zuciya ta hanyar rage cholesterol a jiki.
7.tana kara lafiyar dasashi da kare hakora.
8.tana saukaka yawan laulayin ciki, da yawan amai da yawan tashin zuciya.
10.tana maganin tsutsar ciki.
11.tana kara ma idanu lafiya
12. Tana kara lafiyar ciki da saukaka bahaya
13.tana maganin kumburi da maganin ciwon ga babuwa
da fatan zamu rinka shan abarba akai akai. Kuma Allah temaka mana amin